KannyWood

BA NA KARBAR KUDI IDAN ZAN SAKA DUK WANI JARUMI A CIKIN IZZAR SO – LAWAN AHMAD

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An dade ana ta yada jita jitar cewar duk wani jarumi da zai fito a cikin fim din Izzar so, to babu makawa sai Furodusan fim din Lawan Ahmad, ya karbi kudi a wajen sa musamman ma Jarumai mata wadanda a kullum su ne su ke so a rinka ganin fuskar su, don haka duk abun da aka bukata daga gare su za su bayar domin su Sami biyan bukatar ta su.

A kan haka ne a ke ganin saboda karbuwar da fim din Izzar so ya yi don haka ne mata su ke ta rububin neman a saka su a cikin fim din, yayin da shi kuma Lawan Ahmad a ke zargin sa da cewar yana karbar kudi a kalla daga dubu goma zuwa dubu Ashirin domin ya saka su a cikin fim din.

Sai dai a lokacin da muka ji ta bakin Lawan Ahmad dangane da wannan zargi da a ke yi masa. Ya karyata maganar, in da ta ke cewa, “Duk maganar da a ke fada muna karbar kudi a wajen jarumai kafin mu saka su a cikin fim din Izzar so to ba gaskiya ba ne domin idan muka tashi aikin mu, muna neman jarumin da ya dace da rol din da za mu yi, don haka babu maganar karbar kudi sai dai wanda ya dace a kan rol din. ”

Ya Kara da cewa” Akwai tsarin da mu ke da shi domin kawo gyara ga kamfanin mu da kuma masana’antar fina-finai ta Kannywood, don haka duk wanda zai yi fim a kamfanin mu to muna da dokoki da mu ke da su, don haka mutum zai sayi Fom ya cike domin mu tabbatar, daga ina ya ke kuma menene asalin sa, domin gudun saka kan mu a cikin matsala da ma ita kan ta masana’antar fina-finai ta Kannywood, don haka kudin da mu ke karba na sayen Fom ne ba Wai don jarumi zai fito a cikin Izzar so ba. “

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Source link

Related Articles

124 Comments

  1. Pingback: stromectol tired
  2. Pingback: plaquenil for pain
  3. Pingback: stromectol
  4. Pingback: stromectol 400 mg
  5. Pingback: ivermectin drops
  6. Pingback: ivermectin 12mg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button