Labarai

Babbar Tashar Lantarki ta durƙushe karo na bakwai cikin 2022

Manyan biranen Najeriya ciki har da Babban Birnin Tarayya sun afka cikin duhu daga ranar Laraba, yayin da Babbar Tashar Lantarki ta durƙushe.

Kamfani Raba Ƙarfin Wutar Lantarki ne ya sanar da durƙushewar wajen ƙarfe 11:00 na rana.

Durƙushewar ranar Laraba ita ce ta bakwai a cikin 2022. Gwamnatin Najeriya ta ɗora laifin a kan ƙarancin gas ne ke yawan haddasa jefa ilahirin biranen ƙasar nan cikin duhu. TCN ne ke kula da samar da ƙarfin wuta a faɗin ƙasar nan da ƙasashe maƙwautan da Najeriya ke sayar wa wutar lantarki.

Durƙushewar Lantarki Cikin Yuni : Tashar Wutar Lantarki ta Ƙasa ta durƙushe karo na shida cikin 2022.

Manyan biranen Najeriya sun afka cikin duhu, yayin da Babbar Tashar Wutar Lantarki ta Ƙasa ta sake durƙushewa a ranar Lahadi.

Kamfanonin Raba Wutar Lantarki sun yi sanarwar durƙushewar babbar tashar da yammacin Lahadi, inda su ka ce “durƙushewar ta sake faruwa ne wajen 7 na yamma.

Lamarin ya jefa kusan dukkan manyan biranen Najeriya cikin duhu, ciki kuwa har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wannan ne karo na shida da durƙushewar ta faru, duk da dai wasu rahotanni sun tabbatar da cewa durƙushewar ta fi sau shida a cikin 2022.

Jaridar Punch ta ce sau 17 babbar tashar da durƙushewa a cikin 2022.

Gwamnatin Tarayya ta ɗora laifin kan rashin kulawa daga ɓangaren ma’aikatan tashar da kuma ƙarancin gas.

Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Shiyyar Jos, wato Jos Electricity Distribution Plc, ya yi amfani da shafin sa na Facebook ya sanar wa kwastomomin sa batun lalacewar.

“Mahukuntan Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Jos na sanar da jama’a cewa matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da Ita, ta faru ne saboda durƙushewar babbar tashar wutar lantarki ta ƙasa.” Haka Babban Jami’in Sadarwa na kamfanin, Friday Elijah ya bayyana a shafin Facebook ɗin.

“Amma dai za mu dawo da hasken lantarki da zarar an gyara nan ba da daɗewa ba.”

Shi ma kamfanin raba hasken lantarki na Enugu ya yi irin wannan sanarwa, inda ya ce babbar tashar ta durƙushe wajen ƙarfe 6:49 na yammacin ranar Lahadi, 12 Ga Yuni, 2022.”

Shi ma kamfanin raba hasken lantarki na Legas, Eko Electricity Distribution Company Plc, ya ba kwastomin sa haƙuri, kamar yadda na Jos na Enugu ya yi. Hakan nan shi ma KEDCO na Kaduna ya yi irin wannan sanarwar, ta bakin Jami’in Yaɗa Labarai na su, Abdulazeez Abdullahi.

Ministan Harkokin Makamashi, Abubakar Aliyu ya ce Gwamnati na nan na bakin ƙoƙarin ganin an inganta tare da ƙara yawan wutar lantarkin da ake samarwa.

Ita ma dai gwamnatin Buhari ta bi sahun sauran gwamnatocin baya, domin ita ma ta kasa cika alƙawarin samar da ingantacciyar wutar lantarki.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button