Bidiyoyi

Babu abinda da ya hada Khalifa Sanusi da sauya wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna wurin aiki

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi karin haske game da maganganun dake zagayawa musamman a yanar gizo cewa wai Khalifa Muhammadu Sanusi ya na yi wa gwamnatin sa katsalandan kuma shine ya yi sanadiyyar sauya wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna wurin aiki.

‘ Ni ne a jihar Kaduna ake cewa wai babu mai iya juyani, yaya yanzu za ace wai akwai wani da ke juyani har ya sa wai in yi wani abu da ba haka ba.’

A ranar litinin ne gwamnan Kaduna El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinonin da ya sanar da nadin su a makon jiya ciki harda Mohammed Abdullahi wanda aka sauya wa wurin aiki, daga ofishin gwamna zuwa kwamishina a ma’aikatar Kasafin Kudi.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button