KannyWood

Banbancin da ke tsakanin auren Aisha Tsamiya da na Hafsat Idris.

An kafa wani tarihi a masana’antar Kannywood, inda akai wuf da mashahuran jarumai guda 2, kuma a kusan lokaci daya, wato Aisha Aliyu Tsamiya da Hafsat Idris

To yanzu dai kai tsaye zamu iya cewa yin auren sirri ya fara zama ruwan dare a tsakanin jaruman Kannywood musamman mata, domin kuwa Aisha Tsamiya da Hafsat Idris, suma ba a kan su aka fara ba.

Dukkanin wadannan aure guda 2, ta wata fuskar zamu iya cewa sunada kamanceceniya, amma ta wata fuskar kuma ko hanya basu hada ba.

Idan zaku iya tunawa a watannin baya da suka wuce jaruma Zara Diamond tayi wani abu makamancin na Aisha Tsamiya, inda tayi aure babu sanarwa, sannan kuma ta goge dukkan shafukan ta na sadarwa.

Kuma idan kun tuna, Diamond har fitowa tayi tana rokon duk wanda ya bude shafi da sunan ta, akan cewa ya taimaka ya goge, saboda bata bukatar ganin koda hoton ta guda a yanar gizo.

To irin wannan aure na Zara Daimond shine yai kama da irin auren Aisha Tsamiya, amma baiyi kama da irin auren Hafsa Idris ba.

Saboda itama Aisha Tsamiya ta yanke shawarar datse kowacce alaka da take da ita, tsakanin ta da masana’antar Kannywood, shiyasa koda aka daura auren ta ma, bata fito tayi wa mutane godiya ba, kamar yanda Hafsat Idris tayi.

Jaruma Hafsa ta wallafa sakon godiya bayan auren ta wanda take cewa “Assalamu alaikum, ina mika sakon godiya na ga dukkanin masoya Yan uwa, da abokan arziki na fatan alkhairi da suka min. Sai dai inaso nayi magana akan rade-radin dake yawo musamman Bloggers dake ta update akai na cewa mijin da na aura na da alaka da gidan ABACHA. To wannan na gaskiya bane, bashida alaka da su. Na gode”.

Duk da cewa Hafsa Idris itama ta boye zancen auren ta, kamar yanda Tsamiya tayi, amma ita Hafsa bata datse igiyar alaka tsakanin ta da masana’antar ba, kamar yanda Tsamiya ta datse.

To a karshe dai muna addu’a ga dukkan wadannan amare, cewa Allah Ya basu zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajen auren su. Allah Yasa auren ya kasance “Mutu ka raba takalmin kaza” wato Allah Yasa mutuwa ce kawai zata raba su, amin summa amin.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news