KannyWood

Banbancin dake tsakanin AA Zaura da sauran yan takarar Gwamna a Kano.

Shin wai AA Zaura ne yake neman kujerar Gwamnatin Kano, ko kuma kujerar Gwamnatin Kano ce take neman AA Zaura?

Mai neman fadar gaskiya dole ne yaji tsoron Allah, sannan kuma ya zama wajibi ya zurfafa bincike domin tabbatar da cewa gaskiyar ce tsantsa ta fito daga bakin sa.

Hakika talakawa da yawa a Najeriya ba iya a Kano a kadai ba sun fara cire rai, sun fara hakura da cewa za’a samu ci gaba, saboda an dade ana ruwa kasa na shanyewa.

To a daidai wannan gabar ne nake so na tuna wa yan uwa na da wata ayar Qur’ani, wadda a cikin ayar Allah SWT Yake cewa “LAA TAKNADU MIN RAHMATILLAH” Wato KADA KU YANKE KAUNA DAGA RAHMAR UBANGIJI. Wannan kuma shi ya tabbatar da cewa yanke kauna daga rahmar Allah shima kansa saba wa Allah ne.

A wannan lokacin yan siyasa da dama masu neman kujerar Gwamnatin Kano sun baza komar su, kuma a kalla masu neman kujerar sun kai mutum 11. Daga cikin su akwai Sanata Barau Ibrahim Jibrin, Janaral Ibrahim Sani, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, Murtala Sulen Garo, Kabiru Alhassan Rurum, Barista Inuwa Waya, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Muhuyi Magaji Rimin Gado, Injiniya Mu’azu Magaji, Abba Kabir Yusuf da kuma Ibrahim Al-Ameen Little.

Idan kun lura, zakuga bamu sa AA Zaura a cikin jerin sunayen yan takarar ba. To munyi hakane saboda munce masu neman kujerar gwamnan Kano, shi kuma kujerar ce da kanta take neman sa, shiyasa baya cikin jerin wadancan yan takara masu neman kujera ruwa a jallo. Kuma idan kuka ci gaba da kasancewa damu zaku tabbatar da wannan maganar da muka fada kuma a bisa karbabbiyar ingantacciyar hujja.

Mu hadu da ku a kashi na 2, inda zakuji cikakken bayanin banbancin dake tsakanin AA Zaura da sauran yan takarar gwamnan Kano. Nine naku Al-ameen Ibrahim.

Al-ameen Ibrahim (Ra’ayin AA Zaura)


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. Can I just say what a reduction to search out somebody who truly knows what theyre speaking about on the internet. You positively know how one can convey a problem to light and make it important. Extra people need to learn this and understand this facet of the story. I cant consider youre not more well-liked since you undoubtedly have the gift.

  2. Of course, your article is good enough, baccaratsite but I thought it would be much better to see professional photos and videos together. There are articles and photos on these topics on my homepage, so please visit and share your opinions.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news