Nishadi

BBC Hausa ta kaddamar da sabon shiri na YouTube don mata da matasa mai suna ‘Mahangar Zamani’

Mahangar Zamani sabon shiri ne daga BBC Hausa wanda za a rika sakawa a shafin Youtube duk mako daga ranar Asabar 2 ga watan Agusta.

Shirin zai daukin tsawon minti 25.

Wannan sabon shiri an kirkiro shi ne domin bin diddigin muhawarar dake gudana a tsakanin matasa a shafukan yanar gizo musamman wadanda suka shafi al’amuran yau da kullum da wadanda suka shafe su matasa da mata da kuma matsalolin da ake cin karo da su.

Madina Maishanu ce za ta rika gabatar da shirin talbijin din a shafin YouTube a yanar gizo duk mako.

Madina ta kware a harkar aikin jarida da ya fi karkata kan hotuna da bidiyo. Ta bada gudunmawa matuka wajen ingiza mata yin tururuwa wajen bin shafukan BBC Hausa a yanar gizo. Tana daga cikin wadanda suka shiga gaba-gaba a lokacin zanga-zangar kisar George Floyd a fadar gwamnatin Amurka.

Madina ta ce “ Samun wannan dama na gabatar da shirin Mahangar Zamani abu ne da nake muradi kuma Allah ya sa na kai gashi a rayuta. Abin farin ciki game da shirin shine ganin damace na tattaunawa game da matsalolin da ke damun mu da kuma samar da hanyoyin magance su musamman mata da matasa.

Za a saka adireshin da za’a bi don kallo da bin wannan shiri a shafukan Facebook da YouTube din BBC Hausa.

Babban Editan BBC Hausa, Aliyu Tanko yayi karin haske akan shirin inda yace “ Wannan shiri ne da zai baiwa matasa maza da mata damar fadin albarkacin bakunansu game da abubuwan dake gudana a wannan duniya ta mu sannan kuma da basu damar yin muhawara akan wasu muhimman batutuwa.

Shihrin farko zai tattauna ne kan zumunta da alakar malamai da ɗalibai a jami’o’i.

A cikin wannan shiri, za a tattauna irin alakar dake wanzuwa tsakanin malamai da dalibai a jami’o’in Najeriya. Masu saurare da kallo da kuma wadanda za su tattauna akai za su fede biri ne daga kai har wutsiya kan hadari da yadda wannan alaka ta zama tashin hankali ga dalibai.

A shiri na biyu kuma, za a tattauna ne akan fafutukar kare hakkokin mata a Arewacin Najeriya – A wannan shiri za a duba damar da addini ya baiwa mata da yadda maza musamman a Arewa basu daraja su da irin halin matsi da muzgunawa da suke fadawa a hannun mazaje. A wannan shiri za a ji daga bakunan mata da maza.

Za a saka shirin farko na Mahangar Zamani da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar sannan a ci gaba da sakawa sau biyu a wata.

Bi tattaunawar a #MahangarZamani

Domin karn bayani a aika da sako zuwa wannan adireshin. marina.forsythe@bbc.co.uk


Source link

Related Articles

474 Comments

  1. Pingback: 3reuters
  2. Pingback: 2transcending
  3. Pingback: xxx dating sim gay
  4. Pingback: gay dating sit
  5. Pingback: 1strikes
  6. Pingback: gay sex chat rooms
  7. Pingback: gladiator slots
  8. Pingback: zynga slots
  9. Pingback: dgn free slots

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news