KannyWood

Bidiyo. Cikakken bayanin shara’ar kisan Haneefa.

Har yanzu dai duniya tana cikin jimamin abinda ya faru a jihar Kano karamar hukumar Nassarawa, na kisan wulakanci da wani malamin makaranta Mai suna Abdulmalik Tanko yai wa dalibar sa mai suna Haneefa Abubakar, wadda ta kasance yar shekara 5 kacal da Haihuwa.

A halin yanzu dai zamu iya cewa babu inda wannan labari bai shiga ba, domin kuwa ya bazu ta ko ina a kafafen sadarwa na zamani, da kuma dukkan sauran kafofin yada labarai.

Haneefa Abubakar, yarinya ce da ajalin ta ya riske ta a wata irin hanya, wadda babu wanda yai tsammanin hakan zai iya faruwa. Domin malamin ta wanda ta yadda dashi kuma wanda iyayen ta suka bashi amanar ta, shine yai aikata wannan aiki, inda ya sace ta ya azabtar da ita, ya wahalar da iyayen ta dan’uwan ta, sannan kuma yai mata kisan wulakanci. Daga ‘karshe kuma ya nemi kudin fansa a hannun iyayen ta har Naira Miliyan shida.

Hakika wannan abu yayi matukar tada hankalin mutane, kasancewar wadda aka kashe babu ruwan ta, bata san komai ba a wannan rayuwar, amma cikin rashin imani haka kawai aka kashe ta aka raba ta da duniya.

Malamai, talakawa, masu mulki babu wanda baiyi magana ba akan wannan al’amari, inda kowa yake bayyana jimami da bakin ciki, akan abinda ya faru.

Daga cikin malaman da sukai magana, akwai Shek Aminu Ibrahim Daurawa, Shek Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Shek Abdallah Usman Gadon Ƙaya. Da dai sauran manyan malamai da dama.

Shugaban ‘kasar Nigeria Muhammadu Buhari shima da kan sa ya aiko sakon ta’azzara sa zuwa ga iyayen Haneefa, Sannan kuma matar shugaban, wato A’isha Buhari tayi alkawarin tsayawa akan maganar domin tabbatar an hukunta Abdulmalik Tanko.

Shima Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da tawagar sa, sunje har gidan su marigayiya Haneefa domin yin ta’aziyya. Inda Gwamna yace idan aka kawo masa takardar da zai saka hannu, ta zartar a hukunci, ko minti ‘daya bazai ‘dauka ba wajen rattaba hannu.

To a jiya Litinin ne dai aka shiga Kotun Majestret dake gidan Murtala a cikin jihar Kano, domin fara sauraron karar.

Inda shi mai aikata laifin wato Abdulmalik Tanko, aka gurfanar da shi tare da wasu mutane biyu da suka taimaka masa wajen tabbatar da laifin, wato na miji ‘daya mace ‘daya, wadanda sune Hamisu Isyaku da Fatima Jibrin. Inda kuma ana shara’ar ne tsakanin Gwamnatin jihar Kano da wandanda ake zargin su uku.

A lokacin da za’a fara shara’ar, lauyan gwamnati mai suna Barista Musa Lawan, wanda ya jagoranci sauran lauyoyin gwamnati guda goma sha ‘daya. Ya roki Kotu da ta karanto tuhumar cikin harshen Hausa, domin wadanda ake zargin su fahimta, inda a nan take alkalin da ke jagorantar shara’ar ya amince da haka.

To bayan an gama karanto tuhumar, sai aka bada umarnin tisa ‘keyar masu laifin zuwa gidan gyaran hali na Kurmawa dake cikin jihar ta Kano, kasancewar ita Kotun batada hurumin yanke irin wannan hukunci.

To yanzu dai alkali ya ‘daga zaman zuwa ranar 2/2/2022 idan Allah Ya kai mu.

Yanzu kuma ga cikakken bidiyon yanda lamarin ya kasance.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news