KannyWood

Bidiyo. Yanda su Kabiru Na Kwango suka sha gwagwarmaya a farkon kafa Kannywood.

Kannywood dai wata masana’anta ce ta shirya fina-finan Hausa, wadda take a jihar Kano a Arewacin Najeriya. Kuma an kafata a wajajen alif 1999.

Masana’antar ta fitar da jarumai maza da mata da masu yawan gaske, inda wasu da yawa Allah Yai musu rasuwa, wasu kuma suke nan a raya ana ci gaba da damawa da su.

Kadan daga cikin jaruman da suka riga mu gidan gaskiya a masana’antar sun hada da Hauwa Ali Dodo wadda akafi sani da Biba Problem, Rabilu Musa Ibro, Amina Tumba, Ahmad S Nuhu, Ahmad Aliyu Tage, Zainab Booth Sani Garba SK da dai sauran su.

Daya daga manya kuma tsoffin jarumai a cikin masana’antar, wato Kabiru Na Kwango yayi wani karin bayani akan yanda Kannywood ta ‘dakko asali tun daga farko. Da kuma halin da take ciki a yanzu.

Tsohon jarumin ya bayyana haka ne a yayin da amsa gayyata a shirin “Daga bakin mai ita” wanda BBC Hausa take gabatarwa.

A cikin shirin dai ana gayyato jarumai ne sababbi da tsofaffi, inda ake tattaunawa da su, domin sanin wasu al’amura da suka shafe su.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news