KannyWood

Bidiyo. Yanzu-yanzu Kotu taci gaba da sauraron shara’ar Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe Haneefa Abubakar.

A safiyar yau Laraba ne dai aka koma kotu akan shara’ar Abdulmalik Tanko da Haneefa Abubakar, wanda a halin yanzu kowa yana jira yaga yanda shara’ar ta yau zata kasance.

Har yanzu dai duniya tana cike da alhinin mutuwar Haneefa, wadda malamin makarantar Noble Kids, wanda kuma shine mamallakin makarantar ya sace ta, yai garkuwa da ita, ya kuma kashe ta daga ‘karshe.

Bayan kisan nata ne kuma sai suka saka gawar ta a cikin buhu, suka haka rami a wani bangare na makarantar suka binne ta, tare da hadin gwiwar wani abokin sa. Allah sarki.

Hakika mutuwar wannan yarinya tayi matukar tada hankulan mutane, inda kowa yake ta kira ga gwamnatin jihar Kano, akan tayi gaggawar yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

Shidai Abdulmalik Tanko bai wahalar da shara’a ba, wato tun kafin ma akai shi kotu, ya riga ya gama zayyo dukkan laifukan da ya aikata a lokacin da ‘yan jarida suke tambayar sa.

To yau dai shine zama na biyu da aka yi akan wannan shara’a ta Abdulmalik Tanko da marigayiya Haneefa Abubakar. Kuma kamar yanda kuka sani, gwamnatin jihar Kano da kanta, itace take ‘karar Abdulmalik akan laifin sace Haneefa da kuma kashe ta, da ake zargin sa da aikatawa.

Shafin BBC Hausa ya ziyarci kotun da ake shara’ar, inda suka ‘dakko mana abinda yake faruwa. Ga kuma bidiyon nan a ‘kasa.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news