Labarai

BINCIKEN ‘Pandora Papers’: Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji za ta bi waɗanda aka lissafa sun karya dokar biyan haraji

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta bayyana cewa za ta bi diddigi ta hukunta dukkan ‘yan Najeriya da aka kama sun karya dokar biyan haraji a cikin harƙallar ‘Pandora Papers.’

Cikin wata sanarwa da Kakakin FIRS Johaness Woluola ya fitar, ya ce hukumar za ta bi dukkan mutanen da lissafa sun karya dokokin biyan haraji domin a hukunta su.

Daga cikin ‘yan Najeriya da aka rigaya aka lissafa dai akwai tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, Gwamnan Kebbi Abubakar Bagudu, Sanata Stella Oduah, Shugaban Riƙo na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, Bello Koko da Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun da kuma makusantan su.

PREMIUM TIMES za ta ci gaba da fallasa sauran, da ya ke su na da yawan gaske.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Bello Koko ya daɗe ya na takarar saye gidaje da kadarorin birnin Landan har a gwamnatin Buhari.

Yawancin masu karatu ba su san Mohammed Bello-Koko ba. Amma ɗan taƙaitaccen ƙarin bayanin da za a yi yanzu a kan sa, zai sa kowa ya gane cewa lallai ‘biri ya yi kama da mutum.’

Bello Koko shi ne ma’aikacin gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗa shi riƙon Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), bayan cire Hadiza Bala Usman.

Shugaban Riƙon Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya (NPA) Bello Koko, ya shiga cikin ƙazamar ƙamayamaya da ƙaƙububar satar kuɗaɗen Najeriya ya na kartatar da su waje, inda ya ke sayen maka-makan gine-gine da kadarori a birnin Landan.

A ƙarƙashin wannan harƙalla, ya riƙa yin shigar kare-da-fatar-akuya da sunan wasu kamfanoni biyu na Shell, ya riƙa danƙara kuɗaɗen da ake sayen kadarori a Landan.

Gungun ‘yan jarida masu yaƙi Da ɓarayin kuɗaɗen gwamnati a duniya ne su ka bankaɗo wannan ƙazamar harƙallar da ake kira ‘Pandora Papers’.

Bello Koko tare da matar sa mai suna Agatha Anne Koko, sun yi amfani da wani kamfanin ɓoye sirrin maɓarnata, Cook Worldwide and Alemin, su ka yi rajistar kamfani a asirce ta hanyar ɓoye sunayen su, aka sa sunayen bige a matsayin masu kamfanin.

An raɗa wa kamfanin suna Coulwood Limited, mai rajista lamba 1487897.

An sake ƙirƙirar wani kamfanin na bige mai suna Marney Limited a British Virgin Islands, mai lamba 1487944, duk a cikin 2008.

Waɗannan kamfanonin biyu an yi masu rajista duk a rana ɗaya, 19 Ga Yuni, 2008.

Duk da Bello Koko ma’aikacin gwamnati ne, ya kasance daraktan kamfanonin, abin da ya saɓa wa Dokar Aikin Gwamnanti a Najeriya, Sashe na 5 da na 6.

Harƙallar Bello na daga cikin harƙalla miliyan 11.9 da Gamayyar Ƙungiyoyin ‘Yan Jaridar Binciken Ƙwaƙwaf na Duniya (ICIJ) su ke ci gaba da fallasawa bayan sun bankaɗo su.

Jaridar PREMIUM TIMES kaɗai ce cikin wannan ƙungiya a jaridun Najeriya. Kungiyar ta ƙunshi ‘yan jarida 617 daga gidajen jaridu 150 na ƙasashen duniya.

Waɗannan ‘yan jarida sun shafe shekaru biyu su na bicike a cikin harƙallar tare da bin diddigin hanyoyin da ake satar kuɗaɗen, binciko fayil-fayil ɗin wasu shari’un da ake yi na wasu ƙasashe daban-daban.

Wannan fallasar manyan ɓarayin gwamnati ita ce mafi girma da ‘yan jarida su ka taɓa yi daga cikin ƙasashe 117 na duniya.

Kadarorin Da Bello Koko Ya Saya Cikin Landan, A Ƙarƙashin Mulkin Buhari:

Daga cikin kadarorin da Bello Koko ya saya Landan, har da waɗanda ya saya a Landan cikin 2017, lokacin da bai daɗe da zama Babban Darakta a NPA ba.

Sauran kadarorin kuma ya saye su tsakanin 2008 zuwa 2012.

Da farko ya sayi gida mai Lamba 2, Liberty Court, 141, Great North Way, London.

Ya sayi gidan a ranar 20 Ga Okotoba, 2009, ta hannun dillalin FBN UK mortgage.

Ranar 23 Ga Yuli, 2012, ya sayi mai Lamba 62, Manton Road, Enfield, London.

An sayi ɗaya fam 280,000, ɗayan kuma fam 275,000.

Bello Koko ya sake amfani da kamfanin Coulwood a wannan karo, ya sake sayen gidaje uku.

Akwai mai Lamba 62 Corner Mead, Hendon, (NW9 5RD) a ranar 25 Ga Nuwamba, 2008.

Sai gida mai Lamba 37, Redlands Road, Elfield da aka saya a ranar 16 Ga Agusta, 2011.

Lamba 14, Farady House, Aurora Garden, London, shi kuma an saye shi a ranar 3 Ga Mayu, 2017, a wannan gwamnati ta Mahammadu Buhari.

Na farkon an biya fam 205,000, sai na biyu fam 235,000. Sai kuma gidan Hendon da ya biya fam 350,000.

Na Aurora Garden kuwa da ya saya cikin 2017, ya biya lakadan fam 475,000.

Wannan kantamemen gini shi ne babbar kadara mafi girma da Bello Koko ya saya a Landan.

Kuma ya saye ta lokacin mulkin Buhari ɗin nan, ya na aiki a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA).

Kamfanonin harƙallar Bello Koko na cikin waɗanda Hukumar Bibiyar Harƙalla a Birtaniya (FIA) ta kafa wa idon mikiya a halin yanzu.

Kafin Bello Koko ya fara aiki a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, ya kashe fam miliyan 995,000 wajen sayen kadarori a Landan, tsakanin 2008 zuwa 2012 kenan.

Ba a san dalilin da ya sa ya riƙa sayen gidajen da sunan bogi, maimakon sunan sa na gaskiya ba.

PREMIUM TIMES ta aika masa da saƙon tes, domin jin ta bakin sa, har yau bai maido amsa ba.

A ranar 27 Ga Janairu, 2017, Hukumar Binciken Kuɗaɗen Harƙalla (FIA) a Landan ta nemi ƙarin bayanai dangane da ganin sunaye da kuma bayyanar masu kamfanonin da Bello Koko ke harƙalla, tare da neman wasu ƙarin bayanai daga gare su, amma aka yi ta dawurwura da dabur-dabur.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button