Labarai

Boko Haram sun kashe Janar ɗin sojan Najeriya da wasu sojoji uku

Mayaƙan Boko Haram ɓangaren ‘yan ISWAP sun kashe Burgediya Janar Dzarma Zirkusu a yankin Ƙaramar Hukumar Askira Uba, cikin Jihar Barno.

Sanarwar da Kakakin Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce an kashe Zirkusu tare da wasu ƙananan sojoji uku, a lokacin da suke kan hanyar kai gudummawar yaƙi ga sojojin da suka jajirce suka hana Boko Haram shiga Askira Uba.

Sanarwar ta yi jimamin rashin mamatan kuma ta ce amma an yi amfani da Sojojin Operation Haɗin Kai, aka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda tare da kashe da dama a cikin su, ta hanyar yin amfani da jirgin yaƙi, manyan motocin yaƙi da manyan bindigogi samfurin Tashi-gari-barde.

Yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da cewa ta na samun nasara kan Boko Haram, a kwanan nan ‘yan Boko Haram sun kai farmaki ba sau ɗaya ba a kan sojoji da wasu farar hula.

Cikin ‘yan shakaru kaɗan da suka wuce ne Kamar Ali ya rasa ran sa yayin da Bataliya sa ke fafatawa da ‘yan ta’adda.

Makonni biyu da suka wuce kuma an nuno Boko Haram sun kama wasu jami’an tsaron ƙasar nan su biyu kuma sun kashe su.


Source link

Related Articles

9 Comments

  1. 182362 797404Normally I do not learn post on blogs, nevertheless I would like to say that this write-up really pressured me to take a look at and do so! Your writing style has been surprised me. Thank you, quite fantastic post. 886592

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news