Labarai

Buhari ya kafa tarihin nada mace ta farkon jakadiyar Najeriya a Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada mace a karon farko zama jakadiyar Najeriya a kasar Amurka.

Buhari ya na Uzoma Emenike matsayin jakadiyar Najeriya, wadda za ta wakilci kasar a Amurka.

Nadin Uzoma ya zo daidai lokacin da ita ma Amurka ta samu mace ta farko a matsayin Mataimakiyar Shugaban Kasa.

Kafin wannan nadin da Buhari ya yi wa Uzoma, ita ce Jakadiyar Najeriya a kasashen Ireland da Iceland.

An haife ta a kauyen Umukabia-Ohuhu, cikin Karamar Hukumar Umuahia ta Arewa a Jihar Abia.

An tabbatar da cewa a lokacin da ta ke jakadancin a kasahen biyu, ta taka rwar ganin da babu kamar ta a tsakanin dukkan jakadun Najeriya da ke kasashen duniya.

Wannan ne ma ya za Buhari ya sake nada ta a shekarar da ta gabata, duk kuwa da cewa wasu da dama da aka nada tare da ita a wa’adin farko, Buhari bai sabunta masu wa’adi na biyu ba.

Uzoma ita ce ta canji dattijon nan mai shekaru 83, Nsofor, wanda ya mutu ya na Jakadan Najeriya a Amurka.

Nsofor ya taba yin alkalanci a Kotun Kolin Najeriya.

Tuni dai masu lura da al’amurran diflomasiyya na ganin cewa nadin da aka yi wa Uzoma ya canja akalar diflomasiyya a Najeriya.

Ta na daga cikin jakadu 52 da Buhari ya amince da sake nadin su, watanni shida bayan da Majalisar Tarayya ta tantance su.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button