Labarai

Buhari ya naɗa Bashir Ahmad mai taimaka masa kan harkokin sadarwa na zamani ‘SA Digital Communications’

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon hadimin sa kan sabbin kafofin yaɗa labarai mai taimaka masa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, wato ‘Digital Communications’.

Bashir Ahmad na daga cikin hadimai da ministocin shugaba Buhari da suka ajiye aiki domin yin takara a zaɓen 2023.

Sai dai kuma cikin duka waɗanda suka yi murabu, shugaba Buhari ya musanya su da wasu.

Idan ba a manta ba, Bashir Ahmad ya ajiye aiki domin yin takarar ɗan majalisar wakilai ta tarayya. Sai sai kuma bai yi nasara ba a zaɓen fidda gwani da aka yi zargin tafka maguɗi a wajen yin sa.

Bashir Ahmad ya yi fice matuka wajen kare shugaban kasa da gwamnatin shugaba Buhari a tsawon mulkin gwamnatin.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news