Labarai

Buhari zai sauka ya bar wa ‘yan Najeriya gadon sahihin zaɓe, tulin ayyukan raya ƙasa da tarihin inganta matasa -Gambari

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari za a rika tuna shi a matsayin shugaban da ya samar da sahihin zaɓe, ɗimbin ayyukan raya ƙasa da kuma bunƙasa matasa.

Cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa, Patience Tilley-Gyado ta fitar a ranar Lahadi, Gambari ya ce haka ne lokacin da ‘yan ƙungiyar LMI su ka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa.

Gambari ya yaba da yadda Shugaba Buhari ke mutunta doka da tsayawa bisa dokoki ko wa’adin da dokar ƙasa ta gindaya.

Ya ce za a riƙa tuna Buhari dangane da irin nagartaccen ginshiki da tubalin da ya gina don inganta rayuwar matasa da kuma sahihin zaɓe a ƙasar nan.

“Ya sha faɗa ba sau ɗaya ko sau biyu ba cewa tilas ba zai yiwu a canja wa ‘yan Najeriya wanda duk su ka zaɓa ba. Kuma ya sha nanata cewa zai sauka daga mulki daga ranar 29 Ga Mayu, 2023.”

Gambari ya ce Buhari ya na tafiyar da mulki ba irin na almubazzaranci ba, don haka a cewar sa, Najeriya za ta riƙa tuna shi a kan haka bayan saukar sa.

Gambari ya yi wa maziyartan albishir da cewa, “ina ganin kun taki sa’a kasancewa an haife ku a Najeriya. Saboda ƙididdiga ta nuna cewa nan da 2050 Najeriya za ta kasance ita ce ta uku wajen yawan al’umma a duniya, bayan Chana da Indiya.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button