Labarai

CANJIN SHEƘA: Kotu ta ɗage ƙarar neman ƙwace kujerar Gwamnan Zamfara daga hannun Bello Matawalle

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage sauraren ƙarar da aka shigar ana neman kotun ta ƙwace kujerar Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ta maida wa PDP, saboda ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Wasu mambobin PDP na Jihar Zamfara, Sani Ƙaura Ahmed da Abubakar Muhammad ne su ka shigar da ita.

A ranar 17 Ga Yuni su ka shigar da ƙarar, makonni biyu kafin ma Matawalle ya kai ga canja sheƙar.

Sun yi saurin kai ƙarar ce inda su ka ce a bisa doka, tunda Kotun Koli ce ta ba shi kujerar, haramun ne ya ɗauke ta kacokan ya koma cikin APC ya ci gaba da zama a kan ta.

A lokacin sun ce idan zai koma APC, to sai dai ya sauka. Matawalle dai ya koma APC a ranar 29 Ga Yuli.

Yayin da aka koma sauraren ƙara a ranar Juma’a, lauyan masu ƙara, Kanu Igabi ya cire wasu kusassari biyu a cikin buƙatun da ya nemi kotu ta biya wa waɗanda ya shigar da ƙarar a madadin su. Wato su ne inda ya ce kotu ta dakatar da Gwamna da Mataimakin sa komawa APC.

Lauyan ya yi hakan domin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu bai koma tare da gwamnan ba, shi kuma gwamnan ya rigaya ya koma. Kuma ba a saurari ƙarar ba har Matawalle ya koma.

Lauyan Matawalle, Mike Ozekhome bai yi wata jayayya ba, ya amince Igabi ya zare waɗannan buƙata biyu.

Yanzu buƙatar lauya Igabi ta koma neman kotu ta tsige Gwamna Matawalle kenan.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya soke buƙatun guda biyu, sannan ya ɗaya ƙarar zuwa ranar 29 Ga Satumba.

Yayin da za a ci gaba da sauraren shari’ar, masu sharhi na ganin cewa PDP na so a tsige Matawalle ne a bai wa Mataimakin sa Aliyu kujerar, tunda bai bi shi zuwa cikin APC ɗin ba.

Haka kuma wasu na ganin dalili kenan APC ke ƙoƙarin tsige Aliyu daga Mataimakin Gwamna.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Mataimakin Gwamnan Zamfara ke fuskantar barazanar tsigewa.

Siyasar Zamfara ta ɗauki sabon salo, yayin da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ɗin ke ƙoƙarin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu, bisa zargin ya shirya taron siyasa a lokacin da ake cikin alhinin hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

An kuma zargi Aliyu da nuna rashin ɗa’a da cin mutuncin Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara a wani saƙon tes da su biyun su ka yi wa juna.

Ana raɗe-raɗin cewa ‘yan Majalisar Dokoki na shirin yin amfani da waɗannan dalilai su tsige Aliyu, wanda ya ƙi bin Gwamna Bello Matawalle canja sheƙa zuwa APC.

Majalisa ta nemi Aliyu ya bayyana a gaban ta ya bada ba’asin dalilin da ya sa ya yi taro da kuma bijire wa shawarar da jami’an tsaro su ka ba shi.

Sun ce abin da Mataimakin Gwamnan ya yi abu ne mai iya zafafa matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Zamfara.

Kakakin Majalisar Aliyu Magarya ya tabbatar da aika takardar gayyatar kuma ya ce “abin da Mataimakin Gwamna ya yi ba daidai ba ne.

Mamba mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Maru ne ya gabatar da roƙon a gayyato Mataimakin Gwamnan.

Yusuf Alhassan ya zargi Mataimakin Gwamnan da ƙoƙarin haddasa tashin hankali a jihar.

Sai dai Mataimakin Gwamnan ya ce har yau bai amshi takardar gayyatar ba, domin ba ta kai wurin sa ba.

An dai nuno Mataimakin Gwamnan a cikin wani bidiyo ya na cewa babu wanda ya isa ya hana shi shiga Zamfara.


Source link

Related Articles

60 Comments

 1. Hello! I’m at work browsing your blog from my new apple iphone!
  Just wanted to say I love reading through your blog and look forward to all your posts!
  Carry on the excellent work!

 2. When I initially commented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox and now each time a comment is
  added I get three e-mails with the same comment.
  Is there any way you can remove me from that service?
  Bless you!

 3. Link exchange is nothing else however it is only placing the other person’s website link on your page at appropriate place and
  other person will also do similar in support of you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button