Wasanni

CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

Ihu uku masu rugugin ƙara aka kwartsa a ranar Asabar da dare a cikin birnin Kano, kusan a kowace unguwa, a lokaci ɗaya.

Ihu na farko an yi shi a daidai minti na 73, lokacin da ƙungiyar Manchester City ta jefa ƙwallo a ragar Real Madrid. Hakan ya sa ‘yan adawa sun kwartsa ihun murnar za a fitar da Madrid kenan, tunda sai da idan ta jefa ƙwallaye 3 kafin tashi wasan shi ne za ta iya yin galaba kan Man City.

Ihu na biyu bai yi ƙarfin na farko ba. Magoya bayan Madrid ne su ka yi ihun murnar ƙwallon farko da Rodrygo ya jefa a ragar Man City a minti na 90. Saboda sun rigaya sun karaya cewa an fitar da su kawai.

Ihu na uku wanda magoya bayan Real Madrid su ka yi a Kano da sauran manyan birane da dukkan garuruwa na duniya, ya fi ihu na farko da na biyu ƙarfi. Ihun murnar wasa ya koma ɗanye ne shataf, an yi kankankan tsakanin kulob ɗin biyu. Wato za a ƙara masu lokaci kenan.

Ihu na huɗu wanda ya ɗime duniya shi ma magoya bayan Madrid ne su ka yi shi, murnar Karim Benzama ya jefa ƙwallo ta uku, alama ko tabbacin an fitar da Manchester City kenan a wasan kusa da na ƙarshe.

Tsakanin Pep Guardiola Da Yaya Toure:

Wannan shi ne karo na shida da aka fitar da Pep Guardiola a daidai wasan kusa da na ƙarshe a gasar Champions League, tun bayan sa-in-sa ɗin sa da ɗan wasan Afrika Yaya Toure, a lokacin da Pep Guardiola ke koyar da wasa a Barcelona.

Cikin 2010 Pep Guardiola ya sayar da Yaya Toure daga Barcelona zuwa Manchester City, lamarin da bai yi wa Toure daɗi ba, ko kaɗan.

Wani sabon abin takaici ga Yaya Toure, shi ne lokacin da Pep Guardiola ya bar Bayern Munich ya koma koyarwa a Man City kulob ɗin da ya sayar da Toure cikin, sau ɗaya tak ya sa Toure a farkon wasa, kuma sau 10 kacal ya buga wasan Premier na kakar 2017/2018.

Irin yadda Guardiola ya riƙa wulaƙanta Yaya Toure ya fusata ejan ɗin Toure mai suna Dmitri Seluk, har ya ce “mugun-baki da tsinuwar da ‘yan Afrika su ka yi wa Guardiola saboda wulaƙanta ‘yan wasan Afrika, za ta riƙa bin sa yadda har abada ba zai sake cin kofin Champions League ba.”

Shin Tsinuwar Yaya Toure Ta Bibiyi Guardiola?:

Sau 6 Guardiola na zuwa wasan kusa da na ƙarshe bayan ya sayar da Yaya Toure, amma ya na kasa zuwa wasan ƙarshe ballantana ya sake lashe kofi.

Gasar 2009/2010 da 2011/12 ya je kusa da na ƙarshe a Barcelona.

2023/14, 2014/15 da kuma 2015/16 duk Pep Guardiola ya je wasan kusa da na ƙarshe a Bayern Munich. Amma bai dangana da wasan ƙarshe ba.

Sai kuma yanzu a 2021/22 da Real Madrid ta doke shi daidai lokacin tashi daga wasa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news