KannyWood

Cikakken bayanin cutar HIV da AIDS a cikin harshen Hausa.

Hakikan gaskiya sanin wannan cuta yanada mhaimmanci, domin yanda wasu suke daukar cutar kuma suke kallon ta ba haka take ba.

Da farko idan akace HIV to an takaita sunan ne, idan za’a fada a jimlace to shine Human Immunodeficiency Virus
Wato da Hausa ana nufin Cuta mai karya garkuwar jikin dan adam.

Kowanne Dan Adam yanada wasu kwayoyin halitta a jikin sa, wadanda suke da karfin yakar duk wata cuta da take shiga jikin mutane, shiyasa wanda kwayoyin halittar sa suke da karfi zai wahala cuta ta kwantar da shi. To ita cutar HIV idan ta shiga jikin dan Adam tana rusa wannan garkuwa da take taimakon jikin mutum.

Sannan ita cutar HIV idan ba’a daukin matakin da ya dace akanta ba, shine take rikidewa ta koma AIDS, ita kuma AIDS a jimlace tana nufin Acquired Immunodeficiency Syndrome.

Har yanzu dai a bisa doka, babu takamaiman maganin wannan cuta, ma’ana idan ta kama jikin mutum to zai zauna tare da ita ne har karshen rayuwar sa. Sai dai akwai magani wanda yakeda karfin gaske wajen yakar cutar, wanda yake hana katabus, sai dai baya kashe cutar kwata-kwata.

Idan mai dauke da cutar yabi dokokin likitoci, to zai iya kasancewa cikin koshin lafiya, sannan kuma zai kiyaye iyalan sa daga fadawa mummunan hadari.

Daga ina aka samo cutar HIV.

Bincike ya tabbatar da cewa asalin wannan cuta an samota ne daga cikin Gwaggwan biri daga nahiyar Africa. Sai dai ita wadda ta fito daga jikin birin ana kiran ta SIV wato Simian Immunodeficiency Virus. Daga nan sai cutar ta tsallako ta shiga jikin wasu mafarauta a lokaci da suka kama Gwaggwan birin a matsayin naman farauta. Binciken ya tabbatar da cewa wannan al’amari ya faru tun a wajajen shekarar alif 1800s.

Bayan wasu tsawon shekaru sai cutar ta bazu a cikin kasashen Africa da wasu sassa na duniya.

Ta yaya mutum zai san yana dauke da cutar?

Babbar hanya da mutum zai san yana dauke da wannan cuta itace Gwaji, ta hanyar gwaji ne kadai mutum zai san halin da yake ciki.

Alamomin cutar.

Cutar dai tana daukar a kalla sati 2 zuwa 4 kafin ta fara nunawa a jikin mutum. Tazarar lokacin dake tsakanin kamuwa da cutar da bayyanar ta, ana kiran sa Acute HIV Infection Daga cikin alamomin da mutum zaiji a jikin sa idan ya kamu da HIV sun hada da
• Zazzabi
• Kuraje
• Gumin dare
• Ciwon gabbai
• Ciwon makogwaro da dai sauran su.

Wasu mutanen basa jin komai a jikin su a lokacin matakin farko na cutar. Idan kana tunanin cewa kana dauke da cutar, to garzaya asibiti domin a dubaka, domin ita kadai ce hanyar tabbatarwa.

Matakan cutar HIV.

HIV tanada matakai guda 3, wadda take farawa daga matakin farko, sannu a hankali idan ba’a kula da magani ba sai taci gaba taje har matakin karshe. Daga nan kuma labarin bazai dadi ba.

Matakin cutar guda 3 sune kamar haka

  1. Acute HIV Infection (AHI
  2. Chronic HIV Infection (CHI)
  3. Acquired Immunodeficiency Syndrome (AIDS).

Matakin farko wato (AHI) shine wanda ake jin alamomin cutar, sai dai kamar yanda muka fada a baya, ba kowa ne yake jin alamomin cutar ba.

Mataki na 2 wanda shine CHI, kuma ana kiran sa Symptomatic HIV Infection, ko kuma Clinical Latency.
A wannan matakin cutar tana nan, amma kuma batada karfin da zata ruguza garkuwar mutum. Ba lallai mutum yaji wata alama ko kuma ya kamu da rashin lafiya a wannan matakin ba, yana iya yiwuwa mutum ya zauna da cutar tsawon shekaru, ba kuma tare da shan magani ba. Amma wasu kuma basa samun wannan dama, sakamakon rashin karfin garkuwar jikin su.

Amma kuma a wannan matakin mutum zai iya yada cutar zuwa ga wasu mutanen.

Daga karshe akan dai wannan mataki, adadin kwayoyin cutar wanda ake kira Viral Load sai yayi sama, sai kuma kwayoyin halittar da ake kira CD4, sai suyi kasa, sai kuma alamomin cutar su fara bayyana a jikin mutum. Daga nan kuma sai cutar ta tafi matakin karshe, wato mataki na 3.

Sai dai wadanda suke shan magani a lokacin da suke mataki na 2, to bincike ya tabbatar da cewa babu yanda za’ai su hau mataki na 3.

Mataki na uku kuma na karshe. Wato Acquired Immunodeficiency Syndrome wato AIDS.

Wannan matakin shine mafi tsanani a cutar, domin a matakin ne cutar take rikidewa ta koma abinda ake kira Opportunistic Infections, wato matakin da kwayoyin halitta suke dakko hanyar mutuwa murus.

Akan wannan matakin karshen idan ba’a shan magani bincike ya nuna cewa mutum zai iya rayuwa tsawon shekaru 3 kacal.


Source link

Related Articles

One Comment

  1. Undeniably believe that which you stated. Your favorite justification appeared to be on the web the simplest thing to be aware of. I say to you, I definitely get irked while people think about worries that they plainly do not know about. You managed to hit the nail upon the top as well as defined out the whole thing without having side effect , people can take a signal. Will probably be back to get more. Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news