Labarai

Cire ni daga Sarautar Kano ba zai hana ni ci gaba da faɗin gaskiya ba

Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa duk da an cire daga sarauta, zai ci gaba da bayyana gaskiya da faɗin ra’ayin sa wajen kare ƙasa da sake gina Najeriya.

Muhammadu Sanusi wanda shi ne Khalifan Tijjnaniya na Najeriya, ya bayyana haka a Abuja yayin da ya ke magana a wurin da aka yi wata diramar daɓe, mai nuna bayanin cire shi daga sarauta zuwa lokacin naɗa shi Khalifan Tijjnaniya.

Diramar mai suna “Emir Sanusi: Truth in Time”, an nuna ta ne da babban ɗakin taro na ‘Yar’Adua Centre, Abuja a ranar Asabar.

Farfesan tsara wasan dirama, Ahmed Yarima na Jami’ar Redeemer ne ya rubuta diramar, yayin da Joseph Edgar na kamfanin shirya finafinai na Duke of Somolu Productions ne furudusan wasan.

Sanusi ya ce ya na da ƙwarewar da zai iya bayarwa wajen gina ƙasar nan, idan ya yi la’akari da daɗewar da ya yi ya na yi wa ƙasar nan aiki.

Ya ce ya yi aiki a Bankin UBA, First Bank da kuma zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), kuma ya yi Sarkin Kano tsawon shekaru shida, yanzu ga shi Khalifan Tijjnaniya.

Ya ce idan har ya nuna fushi da da-na-sani kan cire shi, to ya yi wa Allah rashin godiya kenan, idan ya yi la’akari da irin muƙaman da ya taɓa riƙewa.

“Ba na jin Allah ya ɗauke wata alfarmar da ya yi min don an cire ni kan mulki. Saboda haka ba ni da wani da-na-sani.”

Furudusan diramar mai suna Edgar, ya bayyana cewa an kashe naira miliyan 40 wajen shirya diramar, wadda ya ce kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane 35 ne su ka ɗauki nauyin rabin kuɗin da aka kashe wajen shirya diramar.


Source link

Related Articles

11 Comments

  1. all slots casino united kingdom reviews, casinos online canada and free
    online slot machines united kingdom, or united statesn slots miami

    Here is my web blog how can i increase my chances of winning roulette [Luann]

  2. major poker in canada, african new zealandns gambling in vegas and usa slot festival, or free online poker machine games australia

    Feel free to surf to my web page best way to play craps at casino (Nate)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news