Labarai

DAJI ZAFI BIRNIN BA SAUƘI: Gwamnatin Buhari ta yi ƙarin kuɗin wutar lantarki asirce

Hukumar Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayar da umarni a asirce ga kamfanonin raba wutar lantarki (Disco) su shida cewa su yi ƙarin kuɗin wuta tun daga farkon watan Fabrairu, 2022.

Gwamnatin Tarayya ce ta bayar da umarnin ƙarin kuɗin wutar, wanda ya fara aiki ba tare da sanin ‘yan Najeriya ba, tun daga cikin watan Fabrairu.

NERC ta ce ƙarin ya zama dole idan aka yi la’akari da ƙarin wutar lantarkin da kamfanonin Disco ɗin ke rabawa a cikin ƙasar nan.

Wasu takardun bayanai da Shugaban NERC Sanusi Garba da Mataimakin sa Musiliu Oseni su ka sa wa hannu a ranar 29 Ga Disamba 2021 ne ya tabbatar da ƙarin.

Kamfanonin shida sun haɗa da PHEDC, KEDC, KEDC na Kaduna, JEDC, IKEDC da IBEDC.

NERC ta ce ƙarin ya zama wajibi saboda tsadar gas, tashin farashin kayayyaki a ƙasar nan, tsadar dalar Amurka da sauran su.

A ƙarƙashin wannan ƙarin, kWh 1 na lantarki da ake biyan naira 50 a cikin Janairu 2022, tuni ya koma Naira 54/kWh tun daga Fabrairu.

Yayin da wasu jihohin da ke biyan Naira 56, yanzu Naira 60 su ke biya.

Fiye da shekaru 30 kenan ana fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya.

Ta kai kowace jam’iyya ke neman mulki sai ta yi alƙawarin samar da wadatacciyar wutar lantarki, amma har yau lamarin ya zama tatsuniya.

APC ta yi kamfen da alƙawarin samar da wutar lantarki cikin 2014 kafin ta kafa mulki.

Bayan ya zama Shugaban Ƙasa, Buhari ya ƙaddamar da aikin samar da wuta a Mambilla.

Sai dai kuma aikin ya zama har gara tatsuniya, yayin da bayan shekaru uku aka gano ko filin dajin da za a yi aikin ma ba a share ba.

Kafin nan kuwa, miliyoyin ‘yan Najeriya sun yi tsammanin an kusan kallama aikin. Ashe ko bulo inci 9 guda ɗaya tal ba a gina a wurin ba.

Bisa dukkan alamomi kuwa haka Buhari zai sauka daga mulki cikin 2023 bai cika alƙawarin aikin tashar wutar Mambilla ba.


Source link

Related Articles

4 Comments

 1. Thanks for some other informative site. The place else may I
  get that kind of information written in such a perfect means?
  I’ve a challenge that I’m just now running on, and I’ve been at the look out
  for such info.

 2. I all the time used to study paragraph in news papers but now
  as I am a user of net therefore from now I am using net for
  articles or reviews, thanks to web.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button