Labarai

DAKATAR DA TIWITA A NAJERIYA: Muna tare da gwamnati dari bisa dari – Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC ta bayyana jin dadinta da goyon baya ga shawarar da gwamnati ta dauka na dakatar da Kamfanin Tiwita a Najeriya.

APC ta ce wannan abu yayi daidai domin Tiwita ta zama annoba a Najeriya.

” Tiwita ya zama annoba a Najeriya, shafin ya zama dandalin yada labaran karya da ba masu neman tada zaune tsaye a kasar nan wuri da zasu riki kulla munafunci da yada bala’i a kasa. Shafin ke basu dama suna kantara karairayi kan shugabannin da kasa. Ya kai ga idan ba haka a ka yi wa Kamfanin ba yana gab da gungura kasadari bisa dari r nan zuwa balbalin bala’i.

” Muna tare da gwamnati dari bisa dari kan wannan shawara. Dole ayi irin haka idan ana so a samu zaman lafiya a kasar nan.

Kamfanin Tiwita da ke yanar gizo ya bayyana cewa kada ƴan Najeriya su wani damu da dakatar da dandalin daga aiki a kasar, cewa za su tabbatar mutanen Najeriya sun ci gaba da mu’mula da su duk da dokar da gwamnatin Najeriya ta saka.

” Abinda gwamnatin Najeriya ta yi ya saɓa da dama da mutane ke dashi na watayawa da sanin duk abinda suke so na kafafen sada zumunta na zamani. Zamu tabbatar ƴan Najeriya ba su gagara shiga shafin mu ba”.

Sai dai tun da farkon yinin Asabar Ministan Shari’a Abubakar Malami ya gargadi ƴan Najeriya da kakkausar murya cewa duk wanda ya karya dokar dakatar da tiwita da Najeriya ta yi, zai fuskanci hukuma.

Malami ya ce an saka doka a kasa kuma dole abi doka, saboda haka idan wani ya ci gaba da amfani ko aiki da dandalin Tiwita, zai fuskanci tuhuma daga gwamnatin Najeriya.

Ministan ya umarci hukumomin da abin ya shafa su tabbata sun bi avun sauda kafa domin tabbatar da babu wanda ya karya dokar daina amfani da Tiwita a kasar nan.

Dakatar da Tiwita a Najeriya

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, Olumide Akpata, ya kalubalanci gwamnatin Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta gaggauta janye dakatar da Tiwita da ta yi ko su hadu da ita a kotu.

Idan ba a manta ba Kungiyar SERAP ce ta fara bayyana rashin jin dadin kan dakatar da Tiwita da gwamnatin tarayya ta yi ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya din haramtacce ne.


Source link

Related Articles

1,781 Comments

 1. Its lіke you rread my mind! Yоu appear to know a
  lot aƅout this, lіke you wrote tthe book in іt
  oor sοmething. Ι think that yоu could do witһ a feᴡ pics tto drive the message
  һome a bit, ƅut іnstead ߋf that, thіs is wonderful blog.
  An exellent rеad. І will defіnitely Ƅe Ƅack.

  Feel free tօ surf tߋ my page :: home phone service

 2. Hello, I think your website might be having internet
  browser compatibility issues. Whenever I take a look at your
  site in Safari, it looks fine however, when opening in I.E., it has some overlapping issues.
  I merely wanted to provide you with a quick heads up! Other
  than that, great website!