Nishadi

Dalilan da su ka sa matasa ba su ganin darajar mulkin dimokraɗiyya a yanzu -Gbajabiamila

Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya bayyana dalilin da ya ce su ne su ka sa matasan yanzu ba su ganin mulkin dimokraɗiyya da kima ko wata daraja.

Da ya ke jawabi wajen ƙaddamar da taron bai wa matasa 74 horon sanin makamar aiki, Gbajabiamila ya ce matasan yanzu har yau ba su ga wani ƙaƙƙwaran tasirin da dimokraɗiyya ta yi a rayuwar su ba. Shi ya sa ba su san wani muhimmancin da ta ke da shi ba, ballantana har su riƙa yi mata kallon wani tsari mai daraja.

Ya ce akwai buƙatar Najeriya ta samu shugaban zai tabbatar wa matasa cewa mulkin dimokraɗiyya shi ne mulki mafi cancanta da kuma dacewa.

“Matasan yanzu ba su san zamanin mulkin sojoji ba. Shi ya sa ba su san darajar mulkin dimokraɗiyya ba. Amma akwai buƙatar su samu shugaban da zai nuna wa matasa a aikace cewa mulkin dimokraɗiyya ne mafi cancanta ga rayuwar su.

“Su fa matasan yanzu ba su san jiya ko shekaranjiya ba. Ba su san mulkin sojoji ba, ba su san illar mulkin sojoji ba. To kuma sun yi rashin sa’a ba a gamsar da su yadda za su yarda cewa dimokraɗiyya ce mafi tasiri ba. Saboda haka za su yi amfani ne da zahiri su auna zahirin abin da su ka sani kuma su ke gani.” Cewar Gbajabiamila.

Sama da shekaru 12 kenan Najeriya ke fama da matsalolin Boko Haram, sannan kuma ga ‘yan bindiga da su ka hana miliyoyin jama’a zama lafiya.

A cikin birane kuma matasa na fama da barazanar lalacewar ilmin zamani, dalilin yajin aikin malaman jami’o’i.

Sannan kuma miliyoyin matasa na fama da rashin aiki, bayan sun shafe shekaru da kallama jami’o’i.

Wata barazana da matasan ke ci gaba da fuskanta, ita ce idan ba ka da wani babba a sama, to ko ka cancanci a ɗauke ka aiki, ba za ka samu ba. Sai dai wanda ke da ɗaurin gindi zai samu, ko da kuwa bai cancanta ba.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. I got what you intend, regards for posting.Woh I am glad to find this website through google. “I was walking down the street wearing glasses when the prescription ran out.” by Steven Wright.

  2. Have you ever considered publishing an e-book or guest authoring on other websites? I have a blog based upon on the same topics you discuss and would really like to have you share some stories/information. I know my viewers would enjoy your work. If you are even remotely interested, feel free to send me an email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button