Labarai

Dalilin ayyukan da Buhari ya jijjibga a yankin kudu, ba sai APC ta yi kamfen a zaben Anambra ba

Dan takarar gwamnan jihar Anambra na jami’iyya APC kuma sanata mai wakiltan Anambra ta Kudu Andy Uba ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba sai ta yi kamfen a jihar ba saboda ayyukan da Buhari ya jibjibga a fadin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya.

Uba ya fadi haka ranar Juma’a a garin Awka a zaman da uwar Jami’iyyar ta jihar ta yi da shugabannin jami’iyyar na kananan hukumomi 21 na jihar.

Ya ce ayyukan da gwamnatin Buhari ta aiwatar a jihar da jihohin yankin Kudancin kasar nan ya isa jami’iyyar ta yi nasara a zaben gwamnan jihar.

Uba ya ce daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi shine gina gadar Neja wanda har yanzu ana gina ta.

Bayan haka sanata Uba ya roki wadanda a ka sami sabani da su a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi wanda ya yi nasarar samun takarar.

“An yi zaben fidda gwani kuma an kammala yanzu lokaci ne da za mu hadu mu dunkule wuri daya domin yin nasara a zaben dake gaba, wato zaben gwamna ranar 6 ga Nuwamba.

“Idan har muka yi nasaran da da yawa daga cikin mu za su zama sanatoci wasu su zama ‘yan majalisar wakilai da dai sauran su.

Uba ne dan takarar APC, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Charles Soludu ne zai fafata da shi a APGA, shi kuma Valentine Ozigbo dan takarar kujerar na PDP.


Source link

Related Articles

12 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button