Labarai

Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar dakatar da Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, kwana ɗaya bayan da Hukumar EFCC ta kama shi, dangane da zargin sace aƙalla naira biliyan 80 ta hanyar kwangilolin bogi.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ce ta fitar da sanarwar dakatar da Idris a ranar Laraba, inda a cikin sanarwar aka ce “an dakatar da Idris ba tare da za a riƙa biyan sa albashi da alawus-alawus ɗin sa ba.

EFCC ta damƙe Idris a Kano a ranar Talata, inda daga can aka sako shi a jirgi, zuwa Abuja.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ana zargin salwantar maƙudan kuɗaɗe a hannun Idris, kimanin naira biliyan 80, waɗanda aka riƙa waskewa da su da sunan ayyukan kwangiloli, amma fa na bogi.

Majiya ta ce an gano cewa an riƙa sayen maka-makan kadarori da kuɗaɗen a Kaduna da Abuja.

Wata majiya kuma ta ce ana binciken wasu mutane da ke da alaƙa da Ahmed Idris duk dai a kan salwantar maƙudan kuɗaɗen.

Cikin sanarwar dakatar da shi, an umarce shi kada ya kuskura ya leƙa ofishin sa. Kuma kada ya yi wata mu’amala da ko da ɗaya daga cikin ma’aikatan ofishin sa.

“An yi haka ne domin kada ka yi katsalandan a cikin binciken da ake yi maka.”

EFCC ta ce ta daɗe ta na bibiyar binciken harƙallar, kuma hukumar ta sha gayyatar Idris domin zuwa hedikwatar ta yi mata ƙarin haske, amma ya yi biris kamar bai san ana aika masa wasiƙun gayyatar ba.

A yanzu dai Idris na hannun EFCC, wadda kuma ta buga hotunan wasu kantama-kantaman gine-gine 17 da ta yi zargin duk daga cikin biliyan 80 ɗin ne Idris da iyalan sa su ka mallake su.


Source link

Related Articles

13 Comments

 1. CANMED uluslararası tecrübesi ile tropikal ürünleri en kısa
  sürede ve ekonomik olarak ülkemiz pazarına
  sunmaktadır. Kuruluşumuzun kalite standartları için buraya tıklayınız.
  Hergün bir.

 2. Added by erotiksinema on. Ev hanımı konulu sex filmi izle.
  Zara ve Pascal evleneli çok uzun bir süre olmamıştır ama olgun ev hanımı Zara, zengin kocasını aldatmaya karar verir.
  Çünkü kendisi aldatılmaktadır ve oğlunun sınıf arkadaşı kendisine çok seksi bakışlar
  atmaktadır. Zara kocasını kaçamak ilişki.

 3. Hey there! I know this is sort of off-topic but I needed to ask.
  Does operating a well-established website such as yours take a massive amount work?
  I am brand new to writing a blog however I do write in my diary everyday.
  I’d like to start a blog so I will be able to share
  my own experience and views online. Please let me know if you have any recommendations or tips for new aspiring blog owners.
  Thankyou!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button