Labarai

Dalilin da ya sa gayu da ‘yan matan Abuja suka fi gane wa saka gwanjo maimakon sabbin kaya

Wasu mazaunan babban birnin tarraya Abuja sun bayyana cewa sun fi gane wa saka kayan gwanjo wanda aka fi sani da ‘Okrika’ mai makon sabbi saboda sun fi aminci da dadewa, sannan kuma sun fi sauki farashi.

Mazauna garin Abuja sun bayyana ra’ayoyinsu game da saka gwanjo a tattaunawar sanin ra’ayoyin mutane wanda kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

Wata mazauniyar Iyanya Grace Ike ta bayyana yadda take amfani da kayan gwanjo daga ita har ‘ya’yan ta saboda arha da amincin da kayan gsuke da shi.

“Abin da na fi so game da kayan gwanjo shine yadda kane zai iya saka rigan wansa idan ya yi kadan.

“Sannan idan har mutum na bukata ya samu kayan gwanjo masu kyau kamata ya yi mutum ya buga sammako zuwa kasuwar dai-dai ana bude beli sabbi masu kyau masu aminci a farashin mai sauki.

Wata daliba kuma mazauniyar Karu Kadijat Idris ta ce tana siyan kayan gwanjo saboda arha da yadda yake da saukin samu. Sannan kuma a kwai saukin al’amari.

Ma’aikaciyar banki Kadijat Idris ta ce kayan gwanjo musamman jaka da takalma sun fi aminci saboda mutum zai dade yana amfani da su.

Masu siyar da gwanjo a kasuwa

Wata maman Ebuka dake siyar da gwanjo a kasuwar Utako ta ce baya ga wannan kasuwa tana zuwa wasu kasuwannin a garin Abuja domin siyar da gwanjo.

“Ina zuwa kasuwar Mararaba ranar Laraba, kasuwar Madalla ranar Alhamis da kasuwa Garki ranar Juma’a don siyar da kaya wa kwastamomi na.

“Ba talakawa kadai ne ke siyan gwanjo ba har da masu kudi komai dai ya danganta da irin abin da mutum ke so ne.

Gargadi

Wani likita Martins Magaji ya gargaddi mutane kan yin amfani da kayan gwanjo musamman kayan mata domin kare lafiyan su.

“Mata na iya kamuwa da cututtuka musamman idan suna saka kayan da wata ta saka.

Magaji ya yi kira ga mutane musamman mata da su tabbatar sun wanke duk kayan gwanjon da suka siyo kafin su saka a jikinsu domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news