Labarai

DALILIN DA YA SA NA NEMI ARCEWA KWATANO: Daga ni sai N3,500 lokacin da aka gaya min mata ta ta haifi ‘yan hudu

Wani magidanci mai shekara 37 dake koyan kasuwancin siyar da tayoyi a jihar Legas Cissé Abdullahi ya yi kira ga gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu da sauran mutanen Najeriya da su tallafa masa wajen kula da ‘ya’yan sa ‘yan hudu da matarsa ta haifa.

Abdullahi dake zama a Kumapaji Phase 3, Baale Bus Stop, Oko-Afo a Olorunda LCDA, ya ce bashi da komai illa naira 3,500 dake aljihunsa.

Ya ce baya ga haka dakin da yake zama tare da matarsa Sekinat ba zai dauki jarirai hudu ba.

Abdullahi ya ce ya samu labarin haihuwar matarsa ranar Litini a hanyar dawowa gida daga shagon koyan kasuwancin tayoyi da yake zuwa

“ Labarin haihuwan mata ta albashiri ne mai kyau amma daga na fara tunanin yadda zan kula da wadannan yara sai hankali na ya tashi.

“Da muka je daukan hoto ‘yan biyu aka ce za ta haifa amma sai gashi ta haifi ‘yan hudu. Da na ji haka ne sai kawai na yanke shawarar in waske zuwa Kwatano, kasar Benin kawai in gudu.

“Da misalin karfe 9 na daren Litini zan tsallaka boda kenan zai wani abokina ya ganni ya tsayar da ni.

“Tun da na dawo gida wannan abokin nan ne ke taimaka mun

Ya ce har yanzu Sakinat na babban asibitin Badagry ba a sallame su ba saboda fida aka yi mata.

Bayan godiya ga Allah da tayi ta ce wannan haihuwa shine na farko kuma Allah ya azurtatat da ‘ya’ya hudu.

Ta kara da cewa lallai mijinta na cikin halin kunci da talauci, yana matukar bukara taimako daga ‘yan Najeriya.


Source link

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news