Labarai

Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

Ɗan majalisan dake wakiltar Kabba/Buni a majalisar Tarayya, Tajuddeen Yusuf ya kada fitaccen ɗan siyasa Dino Melaye a zaɓen fidda gwani na kujerar sanata.

An gudanar da zabukan kujeru sanata da na majalisar wakilai ta tarayya ranakun Litinin da talata.

A zaben farko da aka yi an yi canjaras wato kunnen doki inda Dino da Yusuf suka samu ƙuri’u 88 kowannen su.

Bayan haka sai aka sake yin zaɓe. Anan ne fa Honarabul Yusuf yayi wujiwuji da Dino.

Yusuf ya samu ƙuri’u 163 shi kuma Dino ya samu ƙuri’u 88.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaɓen, Dino ya ce an yi masa taron dangi ne.

” Ban taɓa ganin taron dangi irin wanda aka yi mini ba kawai don a kada ni. Ina taya Yusuf murnar nasarar da ya samu.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button