Labarai

Dogara ya fa ruɗe, Atiku ya ke wa aiki a boƴe, ya na ta wani tsalle-Tsalle – APC

Kakakin kwamitin kamfen din shugaban Kasa na APC, Bayo Onanuga ya zargi tsohon kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara da yi wa Atiku Abubakar aiki da sunan wai yana fushi da zaɓin musulmi da Tinubu yayi mataimakin shugaban kasa.

Onanuga ya ce ” Tun da Dogara ya rasa kujerar zama mataimakin Shugaban Kasa na APC , ya zauce, kullum za ka ji shi a can ya na korafin da babu tushe.

” Sai ya tattaro wasu da tuni an yi sallama da su a jam’iyyar, wai ƴan APC ne amma basu tare da Tinubu. Dukkan su ƴan koron Atiku ne, ba su a APC.

” Tun bayan rasa wannan kujera na mataimakin shugaban kasa na Tinubu, Dogara ya ke faɗin maganganun da basu dace ba, ya maida abin addini, kullum sai faɗefaɗe da karauniya kawai.

A karshe Onanuga ya ce Tinubu ne zai yi nasara a zaɓen shugaban kasa mai zuwa, duk wani adawa da su Dogara ke yi shirme ne kawai da tarkacen banza


Source link

Related Articles

One Comment

  1. Nice blog here! Also your website loads up fast! What web host are you
    using? Can I get your affiliate link to your host? I
    wish my website loaded up as quickly as yours lol

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button