Labarai

Dole fa a sake lale, ace wai Najeriya ce kasar da tafi yawan marasa aikin yi a duniya – Atiku Abubakar

Tsohon shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadin sa ga rahoton Jaridar Bloomberg wanda ta fitar ranar Asabar cewa yanzu Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya yawan wadanda ke zaman kashe wando a duniya.

Atiku ya bayyana rashin jin dadinsa ga wannan rahoto yana mai cewa lallai akwai danyen aiki a gaban su.

” Dole fa a sake lale tunda wuri. Ko wadannan rashin zaman lafiya da tsaro da ake fama da shi a kasar nan ya samo asali ne daga rashin aikin yi da musamman matasa ke fama da shi a kasarnan. Sannan kuma ga tabarbarewar ilimi.

” Yara sama da miliyan 13 ne a kasar nan ke ba su makaranta. Dole sai an tsaro hanyoyin da za a ga an maida wadannan yara makaranta idan ko ba haka ba ana tubka ne da warwara.

” Sannan kuma dole a rage tsananin haraji da aka sanya wa kananan yan kasuwa da masu sana’o’i domin su iya cigaba da cinikayya da nada daman kananan masu karfi su shiga harkokin kasuwanci da sana’o’i.

” Bayan haka ina matukar takaicin sake sarka kudade har sama da naira biliyan 600 da za ayi wai fon gyaran matatan mai na Fatakol. Wannan asara da me yayi kama, wai shin masu ba gwamnati shawara ba su tunani da nazari mai zurfi ne. An rika narka wa matatun kudade kenan kuma basu samar da komai.

A karshe Atiku ya bayyana cewa dole fa a hadu wuru guda a ga yadda za a ciyar da kasa gaba.

” A ce mune talauci, mune rashin aikin yi, mune yawan yaran da basu makaranta a duniya, duk gaba daya.”


Source link

Related Articles

66 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button