Labarai

Duk da kokarin da nake yi wa matata, bata gani gorin yau da ban da na gobe

A kotun shari’a dake Magajin Gari a jihar Kaduna ne Muhammad Abdulganiyu ya kai karar matarsa Ma’arufat Ibrahim a dalilin fita dga gida ba da izini ba.

Abdulganiyu ya ce yana son matarsa sannan yana kokarin biya mata bukatunta daidai gwargwado.

Ya ce sai dai a ranar 16 ga Agusta bayan ya fita ya dawo ya iske gidansa a kule da kwado matarsa bata nan.

“Makwabta sun ce mahaifiyar matarsa ce ta zo ta tafi da ita gida.

Ita kuwa Ma’arufat ta ce ta yi yaji daga gidan mijinta Abdulganiyu ne saboda baya biya mata bukatunta sannan kulum cikin yunwa take da a dalilin haka ya sa har ta kamu da ciwon yunwa wato Ulcer.

Alkalin kotun Malam Rilwanu Kyaudai ya umurci ma’auratan bai wa juna hakuri.

Kyaudai ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 30 ga Agusta sannan ya ce ma’auratan su gabatar da iyayensu a wannan rana.

A wata shari’ar kuma wata matar aure mai suna Safiya Muhammad ta nemi kotu ta raba auren ta da mijinta Salisu Saidu bisa dalilin tafiyar sa da yayi ya bar ta da ‘ya’yan su biyu na tsawon shekara daya.

Safiya ta ce akwai lokacin da ta yi tafiya zuwa jihar Kogi neman maganin rashin lafiya da take fama da ita amma duk zaman da ta yi Saidu bai zo ya gaishe ta ba ko sau daya ba.

“Na gaji da zaman a raba auren kawai shine na ke so.

Saidu ya musanta wai yana cin zarafin matarsa inda ya ce yana matukar son matarsa sannan yana kokari wajen biyan bukatun iyalinsa.

Ya ce haka kawai matarsa ta kama hanya ta tafi jihar Kogi ba tare da sun yi fada ba ko kuma ya sake ta ba.

Saidu ya ce yana son matarsa kuma baya so kotu ta raba auren sa.

Alkali Rilwanu Kyaudai ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 5 ga Satumba sannan a wannan rana Safiya ta kawo shaidun da za su tabbatar wa kotun cewa Saidu na cin zarafin ta.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. I have been looking for articles on these topics for a long time. baccarat online I don’t know how grateful you are for posting on this topic. Thank you for the numerous articles on this site, I will subscribe to those links in my bookmarks and visit them often. Have a nice day

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news