Nishadi

El-Rufai ya rantsar da mika sardar girma ga Sarkin Lere Suleiman Umaru

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi tattaki tare da tawagar sa zuwa masarautar Lere domin mika wa sabon sarkin Lere Suleiman Umaru sandar girma a garin Lere da rantsar da shi a matsayin sabon sarkin Lere.

El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna na taya sarkin Suleiman murna sannan kuma ya yi kira ga sarki Suleiman yayi mulki da adalci kamar yadda kawun sa marigayi Sarki Abubakar II ya yi.

Bayan haka ya yi wa mutanen karamar hukumar Lere alkawarin lallai gwamnati za ta kammala ginin wani ɓangaren jami’ar Kaduna da ta yi alƙawarin ginawa kafin karshen wa’adin gwamnati mai ci.

Bayan bikin mika sandar an shirya kasaitaccen bukin Durba a garin Lere inda mahaya suka yi hawa da kayan ado masu burgewa.

Cikin sarakunan da suka halarci wannan taro akwai sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli da sauran, ƴan siyasa, attajirai da aabokan arziki


Source link

Related Articles

8 Comments

  1. Pingback: 3structural
  2. Pingback: gay online dating
  3. Pingback: gay chat recorded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button