Labarai

El-Rufai ya tabbatar wa sarki Muhammadu Sanusi II rawanin Uban Jami’ar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II shugabancin jami’ar Kaduna a matsayin uban jami’ar.

An saka masa alkyabbar jami’ar da hular ta a wajen bukin yaye ɗaliban jami’ar da aka yi a Kaduna ranar Asabar.

Bayan haka a matsayin sa na shugaban jami’ar bayan naɗa shi sai ya jagoranci yaye ɗalibai da aka yi a makarantar.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya naɗa sarki Muhammadu Sanusi uban jami’ar jihar Kaduna tun bayan cire shi da aka yi daga sarautar Kano.

.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button