Labarai

Fani-Kayode ya nemi jami’an tsaro su damƙe Ayu

Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, Femi Fani-Kayode, ya yi kira ga jami’an tsaro cewa ya yi mamakin da har yau ba su kama Shugaban PDP Iyorchia Ayu ba.

Fani-Kayode ya ce tuni ya kamata a ce jami’an tsaro sun damƙe Ayu da mambobin shugabannin PDP waɗanda aka raba wa kuɗaɗen, tunda dai ta tabbata cewa an yi watandar.

Fani-Kayode ya yi wannan kiran a ranar Titinin a shafin sa na Facebook da Tiwita, inda ya ce ya yi mamakin yadda shugaban PDP ya raba kuɗaɗe masu yawa haka.

Mako ɗaya kafin rabon kuɗin, sai da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yi zargin cewa an bai wa Ayu zunzurutun kuɗaɗe har naira biliyan ɗaya.

“Idan Ayu ya isa, ya fito ya ƙaryata ni. Na ce wani ya ba shi naira biliyan 1 a Legas. Ban ce kuɗin gwamnatin Legas ba ne. Amma dai a Legas wani ya ba shi kuɗin. Idan ƙarya na ke yi, shi Ayu ya fito ya yi magana. A lokacin ni kuma zan faɗi sunan wanda ya ba shi kuɗin.” Inji Wike.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda wasu jiga-jigan PDP huɗu su ka maida kuɗaɗen da aka ba su, bayan sun lura da yadda aka riƙa yi masu terere a jaridu da soshiyal midiya.

A labarin wannan jarida ta buga cewa naira miliyan 120 na neman hargitsa PDP.

Aƙalla Shugabannin Kwamitin Zartaswar PDP huɗu ne su ka maida wa jam’iyyar sama da naira miliyan 120 a cikin asusun ta.

Daga cikin su akwai wanda ya maida naira miliyan 28 wasu har naira miliyan 36. Shugabannin PDP sun ce an ba su kuɗin ne da sunan “alawus ɗin gida” ko “kuɗin haya.”

Su huɗun dai kowane ya rubuta wa Shugaban PDP Iyorchia Ayu wasiƙa bayan sun maida kuɗin, su ka ce sun mayar ne saboda an yi masu terere a jaridu cewa sun karɓi cin-hanci.

Wani ɗan Kwamitin Zartaswar PDP ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an rubuta wasiƙun.

Mambobin na NWC da su ka mayar da kuɗaɗen sun haɗa da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Shiyyar Kudu Taofeek Yamma, Olasoji Adagunodo, sai Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Yankin Kudu, Taofeek Arapaja, sai Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu, Dan Orbih da kuma Shugabar Mata ta Ƙasa, Stella Affah-Attoe.

Yayin da Arapaja ya mayar da naira miliyan 36, Adagunodo da Orbih da Effah-Attoe kowacen su sun maida naira miliyan 28.8.

Cikin wasiƙun da su ka aika wa Ayu, waɗanda PREMIUM TIMES ta ga dukkanin wasiƙun, sun bayyana cewa kuɗaɗen sun janyo idon mutane duk ya koma a kan su.

“Mu na sanar da kai cewa kuɗaɗen da aka ba mu sun janyo masa sa-ido daga jama’a, tare da yi mana terere a jaridu, haka Adagunodo ya bayyana a cikin wasiƙar da ya rubuta wa Ayu.

“Saboda haka ina sanar da kai cewa na maida naira miliyan 28,800,000 a cikin asusun banki na PDP mai lamba 1000095003 da ke bankin Globus Bank PLC. Kuma na manna maka kwafin rasiɗi mai tabbatar da shaidar na maida wa PDP kuɗin ta a banki.”

Kamar yadda ya yi, ita ma Effah-Attoe a cikin wasiƙar ta, ta ce yayin da ta ga kuɗi naira miliyan 28,800,000 a cikin asusun ta, ta yi tambaya, amma amsar da aka ba ta daga ofishin Ayu ita ce, kuɗin su na zaman kuɗin hayar shekaru biyu ne aka ba ta, a matsayin ta na mambar Kwamitin Zartaswa (NWC).

Ta ce tun daga ranar da aka tura mata kuɗaɗen mutane ke ta damun ta da kiraye-kirayen waya daga ‘yan gidan su, abokai, ƙawaye, ‘yan jam’iyya da ‘yan jagaliya, su na damun ta cewa an ba ta hasafin ne domin ta goyi bayan shugabancin Ayu, kan rikicin sa da Gwamna Nyesom Wike na Ribas.

Shugabar matan ta ƙara da cewa a jaridu da soshiyal midiya sai terere ake yi da su cewa sun cika aljifai da naira miliyan 28.8.

Dukkan su dai sun nuna cewa lamarin ya zubar masu da mutunci, kuma ya kunyata su.

Sai dai kuma bayan fallasar raba kuɗaɗen ne sai Kakakin Yaɗa Labaran PDP, Debo Ologunagba ya fito ya ce kuɗaɗen ba na cuwa-cuwa ba ne, kuɗaɗen kama gidajen haya ne aka raba wa waɗanda aka bai wa kuɗaɗen.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. Fantastic blog! Do you have any tips for aspiring writers? I’m planning to start my own website soon but I’m a little lost on everything. Would you recommend starting with a free platform like WordPress or go for a paid option? There are so many choices out there that I’m completely confused .. Any recommendations? Thanks a lot!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button