Labarai

FARGABAR KORONA: An gindaya tsauraran sharuɗɗa ga masu kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa

Sakamakon ɓarkewar cutar korona a Fadar Shugaban Ƙasa, Gwamnatin Najeriya ta fito da wasu sabbin matakan ƙa’idoji kauce wa sake kamuwa, waɗanda tilas masu kai ziyara za su cika kafin a bari su shiga fadar Aso Rock Villa.

Premium Times ta buga labarin ɓarkewar cutar korona a Fadar Shugaban Ƙasa da kuma yadda gwamnati ta ɓoye labarin ɓarkewar, har sai bayan da aka fallasa tukunna.

Duk da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa Garba Shehu ya tabbatar da ya kamu da cutar, ya ƙi tabbatar da ƙanuwar sauran hadiman da aka ruwaito cewa su ma sun kamu ba.

Hakan ya nuna yadda ake zaman ɓoye wa ‘yan Najeriya sirri a Fadar Shugaban Ƙasa, tun daga lokacin mulkin marigayi Umaru ‘Yar’Adua har zuwa mulkin Buhari.

Sabbin Ƙa’idojin Shiga Villa:

Da ya ke wa manema labarai jawabi a ranar Lahadi, Shehu ya bayyana cewa sabbin sharuɗɗan dai an kafa su ne domin hana sake ɓullar korona a kusa da Shugaban Ƙasa.

Shehu ya ce ba an kafa matakan ba ne ga gwamnonin da ke don kai wa Shugaban Ƙasa ziyara ko wasu manyan baƙi ba ne kaɗai.

Ya ce an gindaya dokakin ne a kan duk ma wani mai don kai ziyara cikin Fadar Shugaban Ƙasa.

“Tabbas an fito da sabbin dokokin hana sake ɓarkewar cutar korona a Fadar Shugaban Ƙasa. Wato su ne kafa ƙa’idoji ga duk wani mai kai ziyara a fadar, waɗanda tilas sai ya cike su kafin ya samu iznin shiga.

“Duk wani mai kai ziyara a cikin Fadar Shugaban Ƙasa, kai ko da ba Shugaban Ƙasa ɗin zai gani ba, to tilas sai an yi masa gwajin korona a daidai ƙofar shiga fadar.

“A kyauta ake yin gwajin, don haka babu wanda za a ce sai ya biya kuɗi. Amma fa wannan doka ta ɗan wani lokaci ce, ba ta dindindin ba ce. Za a cire dokar da zarar abubuwa sun daidaita. Kuma dama hakan ake yi a fadar gwamnatin ƙasashe da dama.”

Ya ce gwamnati na ci gaba da ƙara jaddada cewa yin allurar rigakafi ce kaɗai maganin hana kamuwa da cutar, kuma ta na kira jama’a su riƙa yin kaffa-kaffa yayin bukukuwan sabuwar shekara.


Source link

Related Articles

18 Comments

 1. 473748 721443This Los angeles Weight Loss diet happens to be an low and flexible going on a diet application meant for typically trying to drop the weight as effectively within the have a a lot healthier lifetime. lose weight 3097

 2. 470284 460765I genuinely dont accept this certain write-up. Nonetheless, I had searched with Google and Ive located out that you are correct and I had been thinking in the improper way. Maintain on creating top quality material comparable to this. 337776

 3. I am really impressed along with your writing talents as well
  as with the format to your weblog. Is that this a paid theme or did
  you customize it your self? Anyway keep up the nice quality writing,
  it is rare to see a nice blog like this one these days..

 4. GÜNDE 432 KAMYON KIYIKIŞLACIK TRAFİĞİNE ÇIKACAK.
  İassos Çevre ve Tabiat Varlıklarını Koruma Yaşatma Derneği de projeye karşı dava açanlar arasında.
  Kurumun avukatlığını yapan Murat Kemal Gündüz, yük yükleme projesinin körfezdeki diğer limanlardan ayrı düşünülemeyeceğine dikkat çekti.
  Liman projesiyle birlikte.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news