Labarai

Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa farin jini shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa ya samu daukaka a siyasa gashi yanzu har ya kai ga zama gwamna.

Gwamna Bala ya ce kusanta da yayi da Buhari da kuma shiga jam’iyyar ANPP da yayi ya sa ya samu nasarar darewa kujerar Sanata a 2007.

” Wannan shine dalilin da yasa nake daraja Buhari matuka sannan kuma sai fa inda karfi na yakare ko a yanzu akan duk wani abu da ya shafe shi ko iyalan sa.

” Dama shine da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Duk abin da suka fito nema ba zan neme shi ba.
Bayan haka kuma a karkashin mulkin Buhari duk wani abu na jihar Bauchi, Buhari ya tabbatar da ya kai gare mu, duk wasu kudade na jihar Bauchi, Buhari ya sa mun kai ga su.

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya wakilci shugaban Kasa Muhammadu Buharia wannan taro.


Source link

Related Articles

4 Comments

  1. Thank you for great content. Hello Administ . Onwin engelsiz giriş adresi ile 7/24 siteye butonlarımızla erişim sağlayabilir ve Onwin üyelik işlemini 3 dakika da halledebilirsiniz. onwin , onwin giriş , onwin güncel giriş , onwin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button