Labarai

Fatan dubban daliban jami’o’in Najeriya na komawa aji ya sake bin ruwa

Kungiyar dalibai ta Najeriya ta gudanar da jerin zanga-zanga a yunkurinta na ganin an janye yajin aikin ASUU da ke cikin wata na takwas.

Fatan dubun dabatar daliban jami’o’in Najeriya ga alama, ya sake dusashewa bayan wata wasikar hukuma ta bayyana cewa gwamnati ta janye umarnin a bude manyan makarantun.

Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta gudanar da jerin zanga-zanga a sassan Najeriya ciki har da rufe harkoki a filin jirgin saman Murtala Mohammed na Lagos, a kokarinta na tilasta janye yajin aikin da malamansu ke yi tsawon watanni.

Gwamnatin Najeriya dai ta janye umarnin ta na cewa shugabannin jami’o’i su bude manyan makarantun nasu, bayan wani hukunci da kotun ma’aikata ta yi a baya-bayan nan.

A cikin wata wasikar hukuma da aka fitar ranar Litinin, Hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa ta nemi shugabanni da ubannin jami’o’i da majalisun gudanarwarsu su bude jami’o’in gwamnatin tarayya bayan rufe su tsawon watanni saboda yajin aikin kungiyar ASUU.

Sai dai, tun kafin dare ya yi, sai Hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa ta sake fitar da wata wasikar inda ta ce gwamnati ta janye umarnin da ta bai wa shugabannin jami’o’i tun da farko.

Wasikar wadda ta karade shafukan sada zumunta mai dauke da sa hannun daraktan harkokin kudi da asusun ajiyar Hukumar kula da Jami’o’i, Sam Onazi ta ce “An umarce ni, na janye wasikar Hukumar NUC mai lamba: NUC/ES/138/Vol.64/135, ta ranar 23 ga watan Satumban 2022, game da wannan batu na sama”.

Babu dai wani karin bayani kan dalilin da ya sa gwamnati ta yi amai kuma ta lashe abinta game da wannan umarni na bude jami’o’i.

The post Fatan dubban daliban jami’o’in Najeriya na komawa aji ya sake bin ruwa appeared first on VOICE OF AREWA.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button