Labarai

GADAGADAR SHIGO DA GURƁATACCEN MAI: Aikin Gama ya gama, an bar Gwamnatin Tarayya da bincike

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta yi gagarimin binciken ƙwaƙwaf domin bankaɗo yadda aka shigo da gurɓataccen man fetur a cikin ƙasar nan.

Ƙaramin Ministan Harkokin Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana wa manema labarai haka a Faɗar Shugaban Ƙasa, yau Laraba, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari dai shi ne Ministan Fetur, kuma a ƙarƙashin Ma’aikatar sa ce aka shigo da wannan gurɓataccen fetur ɗin, wanda za a yi bincike.

Haka kuma a ranar Laraba ɗin ce Hukumar Kula da Haƙo Fetur ta NMDPRA ta bayyana cewa fetur ɗin da ke ajiye a manyan tankunan Najeriya ya ragu daga yawan wanda zai wadaci ƙasa cikin kwanaki 30, zuwa adadin yawan kwanaki 20.

Raguwar ta faru ne saboda an killace gurɓataccen da aka hana sayarwa.

Sylva ya ce za a bayyana sunayen kamfanonin da suka shigo da gurɓataccen fetur ɗin, nan ba da daɗewa ba.

“Ba mu tattauna wannan batu ba a wurin Taron Majalisar Zartaswa. Amma idan kun tuna ai jiya na zo mun gana da Shugaban Ƙasa kan batun. Ba ni ne ya kamata ya bayyana maku sunayen kamfanonin da su ka shigo da gurɓataccen fetur ɗin ba. Amma dai mu na kan bankaɗo su.”

“Ba zan yi saurin cewa komai ba tukunna. Amma dai Gwamnatin Tarayya za ta duba lamarin waɗanda motocin su suka lalace bayan sun sha gurɓataccen fetur ɗin.

“Za a yi gagarimin bincike, kuma ba so na ke ku yi sauri ku yanke hukunci ba. Amma dai za a yi gagarimin bincike domin gano kamfanonin da ke da hannu a ciki, sannan mu dawo mu fallasa maku sunayen su ɗaya bayan ɗaya.

The post GADAGADAR SHIGO DA GURƁATACCEN MAI: Aikin Gama ya gama, an bar Gwamnatin Tarayya da bincike appeared first on Premium Times Hausa.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. You actually make it seem so easy with your presentation but I find this matter to be really something which I think I would
    never understand. It seems too complex and extremely broad for me.
    I’m looking forward for your next post, I will try to get the hang of it!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news