Labarai

GANGAMIN ZAƁEN FIDDA GWANI: APC za ta yi taron gangami ba tare da wakilan cikin gida ba, duk da kotu ta ce sai da su

Jam’iyyar APC za ta yi taron gangamin zaɓen fidda-gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa ba tare da wakilan cikin gida ba, kamar yadda Babbar Kotun Kano ta ce tilas sai da wakilcin su za a yi taron.

APC za ta yi taron ne a ranakun 6 zuwa 8 Ga Yuni, a Abuja.

Babbar Kotun Kano a ranar Juma’a ce ta yanke hukuncin cewa wakilan cikin gida za su iya shiga zaɓen fidda-gwani na ‘yan takara, kamar yadda Dokar Najeriya ta ba su ‘yanci.

Wakilan cikin gida su ne mambobin jam’iyya masu riƙe muƙamin gwamnati na siyasa, waɗanda su ka haɗa da kansiloli, ciyamomin ƙananan hukumomi da mataimakan su, gwamnoni da mataimakan su, shugaban ƙasa da mataimakin sa.

Sauran sun haɗa da Sanatoci, Wakilan Tarayya, Wakilan Jihohi, shugabannin jam’iyya na ƙananan hukumomi 774.

Mai Shari’a A.M Liman ya zartas da hukunci cewar Sashe na 223 na Dokar Najeriya ta ba su damar shiga zaɓen fidda-gwani domin su yi zaɓe.”

Wani Hadimin Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila, mai suna Masijide El-Jibrin Gogowa, Habibu Sani, Bilyaminu Shinkafi su ka shigar da ƙarar a ranar 24 Ga Mayu.

Sun kai ƙasar Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Tarayya da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC.

Kakakin APC Felix Morka ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa za su ci gaba da tsara gangamin su ta hanyar yin amfani da wakilan zaɓen ‘yan takara waɗanda Dokar Najeriya Sashe na 84(8) ya amince da su.

Morka ya ce abin lura kuma shi ne a cikin ƙarar da masu ƙorafin su ka shigar, ba su hada da APC ba.

Sannan kuma ba su maka sunan Shugaban APC Abdullaho Adamu a cikin waɗanda su ke ƙara ba.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news