Labarai

Gargaɗin AB Kwacham Kan magoya bayansa kamar yadda ya wallafa ashafinsa na Facebook

Abu Sadiq Al’Nigeria: National Chairman Arewa Youths Concern Media Forum (AYCMF)

Shawara mai muhimmaci ga yan uwana yan Arewa bisa halin rashin tabbas da muka tsinci kanmu a ciki dumu dumu. halin da yankin mu da al’ummar mu suke ciki ba abune da zamuci gaba da nade hannaye muna gani yana cigaba da faruwa batare da motsawa domin kawo sauyi bane.

Inka tsaya ka karewa abunda yake faruwa a arewa kallo daka fahimci ba sauyin shugaban kasa ko wata Jam’iya bane maganin matsalar. matsalar babba ce tawuce karamin tunanin mu. yadda ruwa yake cigaba da cinyemu kullum al’amarin babu sauki sai karuwa in mukayi sake muka tsaya surutai da saka siyasar son zuciya a dukkan al’amuran mu tofa yan bayan mu ma baza su tsira daga irin kaskancin da muke ciki ba a yanzu.

A yanzu mu yan arewa kaskantattu ne ko shakka babu wulakanci da tozarcin da dan arewa yake kallo a arewa da wajen arewa abun bakin ciki ne da tsoro da tashin hankali ga duk mai hankali da tunani. rashin tsaron da muke ciki munin sa wlh yafi karfin abunda muke bayyanawa a kafafen sadarwa. mutanen mu a yankuna dayawa suna cikin tashin hankali mai girman gaske karancin kishin mu ne yasa muke ganin kaman karamin abune yake faruwa. fitintinu suna cigaba da girma ba tare da meda hankali domin magance su ba tun kafin kowa ya rasa madogara.

Wasu abubuwan bazasu bayyanu a rubutu ba sai dai muyi Kukan Kurciya masu hankalin cikin mu su hankalta susan lalle al’ummar mu tana cikin tashin hankali da rashin alkibila.

SHAWARA: Mataki mafi sauki da zamu fara dauka a dede wannan lokacin da ake daf da ayi zabe asamu sauyin gwamnati lalle ya kamata muyi takatsantsan muyi aiki da hankali muyi siyasa mai tsafta mu cire son zuciya wajen zabo shuwagabannin da zasu mulke mu. mu sani zaben shuwagabanni yanada matukar muhimmaci ayi aiki da hankali kafin yin sa domin duk rayuwar mu a karkashin shugabanci take tafiya.

In muka tsaya bangar siyasa a zahiri da a kafafen sadarwa bamu hankalta ba. lalle damu kara zabo baragurbin shuwagabanni irin wanda suke shugabancin mu a yanzu. wanda da aci gaba da tozartamu batare da abun ya dame su ba. muhimmacin zabe da tasirin sa yafi karfin a fifita son zuciya a cikin sa domin da nagartaccen shugabanci da asamu adalci da adalci ake samun zaman lfy da aminci a tsakanin al’umma. sai an samu zaman lfy da aminci kafin a fara maganar ci gaba ko more rayuwa. yanzu mu ba maganar more rayuwa ake ba maganar a samu zaman lfy da aminci a tsakanin mu ake

A yayin zabe muyi kokari mu duba cancanta da nagartar dan siyasa a kowacce Jam’iya a kowanne mataki. babu ruwan mu da la’akari da jam’iyar sa. in jam’iyun siyasa sukayi zabukan fidda gwani mu dukufa da nazari akan yan takarkarun da suka tsayar domin zabo mutanen kirki ba tare da wai sai sun raba mana motoci ko baburan hawa ba sannan mu bisu da addu’o’i.

In mukace sai wanda dasu raba mana motoci da babura da kudi damu zaba to lalle mu shirya ci gaba da rayuwar kaskanci a karkashin shugabancin su. Muyi kokarin cire son zuciya a harkar zaben shuwagabanni. domin halin da al’ummar arewa take ciki akwai rashin kyakkyawan shugabanci. da munada shugabanci baza a kashe sama da mutane 150 a rana daya bakaji kasar ta rikice an dimauce domin daukar mataki ba. wlh rashin nagartaccen shugabanci ne kawai yake kara rura wutar fitintinun da suke faruwa a Arewacin Nigeria.

Muyi kokarin samar da shugabanci nagari a yankin mu ta hanyar kakkabe gurbatattun yan siyasa wanda gazarwa su tafito fili babu rufa rufa. mu sauya su a dukkan matakai gwamna sanata rep duka babu maganar siyasar uban gida uban gidan ka in bai cancanta kayi kokarin saukakawa kanka da al’ummar da kake rayuwa a cikin ta ka zabo wanda ya cancanta.

#MuyiAikiDaHankali. Ataimaka atura wannan sakon gaba🙏
16/4/2023


Source link

Related Articles

79 Comments

 1. Pingback: 2laundry
 2. Pingback: writing help
 3. Pingback: ivacy vpn
 4. Pingback: cheap vpn
 5. Pingback: avg vpn
 6. Pingback: cheap vpn
 7. Pingback: buy vpn cheap
 8. Pingback: #ИМЯ?
 9. Pingback: dating guide
 10. Pingback: chat-avenue/gay
 11. Pingback: gay lesbian chat
 12. I will right away seize your rss feed as I can not to find your e-mail subscription link or e-newsletter service. Do you’ve any? Kindly allow me recognize in order that I could subscribe. Thanks.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button