Labarai

GARIN NEMAN ƘIBA: Wani matashi ya bindige ƙanin sa a ƙoƙarin gwajin laƙanin bindiga da aka basu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta bayyana cewa tana farautar wani matashi da ya kashe kanensa a jihar, sannan ya arce.

Kakakin rundunar Ajayi Okasanmi wanda ya sanar da haka a garin Ilorin ya ce matashin ya kashe kanensa mai shekara 12 a lokacin da ya ke yin gwajin laƙanin bindiga da wani boka ya basu.

Okasanmi ya ce wannan abin takaicin ya auku a kauyen Dutse Gogo dake karamar hukumar Kaiama.

” Bayan yaran sun karɓo lakanin bindigan sai wan ya dauko bindigar da mahaifinsu mai suna Abubakar Abubakar, ke zuwa farauta da ita, ya danƙara mata harsashi ya fuskanci ƙaninsa wanda shine ya ɗaura shirgegiyar layar da boka ya basu ya danna masa mata.

Nan ko take kanen na sa ya yanke jiki ya faɗi gawa ko shureshire bai yi ba. Daga ganin haka kuwa sai wan ya tattara nasa-inasa ya arce.

Okasanmi ya ce tuni rundunar ta fara farautar matashin domin a hukunta shi.

Daga nan sai yayi kira ga iyaye da su rika sa wa ƴaƴan su ido matuka domin kauce wa aukuwar irin haka.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. Looking at this article, I miss the time when I didn’t wear a mask. casino online Hopefully this corona will end soon. My blog is a blog that mainly posts pictures of daily life before Corona and landscapes at that time. If you want to remember that time again, please visit us.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button