Labarai

GOBARA A PDP: ‘Da na goyi bayan a zaɓi Bafulatani gara na mutu’ – Saƙon Gwamna Ortom ga Atiku

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce da ya goyi bayan zaɓen Atiku Abubakar a 2023, har gara mutuwa ta ɗauki ran sa.

Da ya ke magana a taron cin abincin dare a Gidan Gwamnatin Jihar Benuwai, Ortom wanda ya karɓi baƙuncin sauran fanɗararrun gwamnonin PDP su huɗu, ya ce duk wani ɗan asalin jihar Benuwai idan ya kuskura ya zaɓi Atiku, to ba ya kishin jihar sa ta haihuwa.

Gwamnonin da su ka halarci dinar sun haɗa da Okezie Ikpeazu na jihar Abiya, Seyi Makinde na Jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Ebonyi, sai kuma Nyesom Wike ɗin mai masaukin baƙi.

“Ba zan taɓa zaɓe ko goyon bayan takarar Atiku Abubakar ba. Kuma duk wani ɗan jihar Benuwai da ya zaɓi Atiku Abubakar, to ba mai kishin Benuwai ba ne.

“Ni dai ba zan taɓa goyon bayan a zaɓi kowane Bafulatani ba, saboda su ne ke kashe jama’a a cikin jiha ta ba.

“Duk wanda zai je ya kai wa Atiku gulmar cewa na ce ba zan zaɓe shi ba, to ya je ya faɗa masa.

“Amma ni duk wani wanda ya yi min alƙawarin zai kare mutanen jiha ta, to shi zan zaɓa.

“Atikun me? Babu ruwa na da shi. Ba zan zaɓe shi ba, tunda Bafulatani ne, kuma Fulani ke kashe mutanen jihar mu. Wanda ya zaɓi Atiku Abubakar kuwa to makiyin jihar Benuwai ne.

Dama makonni biyu sai da Gwamna Ortom ya ce Atiku ya fito ya roƙi gafarar sa, ‘Fulani zalla ba za su iya kafa shugaban ƙasa a PDP ba’.

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya yi kakkausan kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar cewa ya fito ya roƙi afuwa daga wurin sa, saboda ya kantara masa ƙarya.

A ranar Laraba ce Ortom ya yi wannan gargaɗin ga Atiku, lokacin da ya karɓi siyasar da ƙungiyar Matasan Jemgbagh su ka je yin zanga-zanga a Gidan Gwamnatin Jihar Benuwai, a Makurɗi.

Ortom ya ce Atiku ya nemi afuwar Ortom, saboda ya ce ‘yan ‘uwan Ortom su na satar wa Fulani shanu a Benuwai.

“Yayin da na ji bayanin sa a labarai, nan da nan sai na tura masa saƙon tes ta WhatsApp, nan take kuma ya ba ni haƙuri.

“Amma sai na ce ya fito ya nemi afuwa, amma ya yi ƙememe ya ƙi fitowa sarari ya nemi afuwa daga wuri na.

“To ni abin da na ke cewa, ba zai yiwu Atiku ya yi wa dattijo kamar ni tsirara a tsakiyar kasuwa ba, sannan mu je gida ya suturta ni a cikin ɗaki.

“Ya shirga min ƙarya, kuma ba zan taɓa lamuntar haka ba. Furucin da ya yi a kai na kalaman ƙiyayya ne,” inji Ortom.

Gwamna Ortom ya ce ba gaskiya ba ne da Atiku ya ce Ortom ɗin ya yi wa Fulani jam’u, ya ce dukkan su ɓatagari ne. Ortom ya ce bai taɓa cewa haka ba.

“Wasu Fulani da dama abokai na ne, kuma na riƙe su amana har ta kai cikin ɗakin kwana na ma sun taɓa shiga. Kuma ni ban taɓa korar Bafulatani ko ɗaya ba.

“Amma Fulani baƙi ‘yan ƙasar waje masu shigowa daga Mali, Mauritania da wasu ƙasashe, su ne ke yi wa mutanen jihar mu ta’addanci.

“Atiku ba ka yi wa mutanen Jihar Benuwai adalci. To ka sani dai Fulani su kaɗai ba za su iya sa ka ci zaɓe har ka zama shugaban ƙasa ba.” Inji Ortom.

Sai dai kuma Ortom ya ce duk da rikita-rikitar da ta dabaibaye PDP, zai yi bakin ƙoƙarin sa domin jam’iyyar ta lashe zaɓen 2023.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. I do not know if it’s just me or if everyone else encountering problems with your blog.

    It appears like some of the text on your posts are running off the screen. Can somebody else please comment
    and let me know if this is happening to them as well?
    This might be a problem with my web browser because I’ve had this happen previously.

    Kudos

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button