Labarai

Gobara ta babbake gidan gogarman Yarabawa da ya ce sai ya gama da Fulani Makiyaya

Gabara ta kone daya daga cikin gidajen gogarman Yarabawa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a cikin tsakar daren Litinin.

Wutar wadda ta tashi misalin karfe 3:00 na Asubahin wayewar garin Talata, ta kone gidan Sunday wanda ke cikin unguwar Soka, a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sai dai a lokacin da wutar ta tashi ba ya ciki, kuma har zuwa yanzu ba a san dalilin tashin gobarar ba.

Gidan ya kama da wuta, kwanaki kadan bayan ya ja zugar matasan da su ka fatattaki wasu Fulani a yankin Ibarapa cikin jihar Oyo.

Lamarin ya kai ga kone gidan Sarkin Fulanin Oyo da ke Igangan jihar Oyo.

Tashe-tashen hankulan da Sunday ya fara tayarwa ya samo asali ne a kokarin sa na korar Fulani daga Oyo.

Taron da Gwamnonin Jihohin Yarabawa su ka gudanar tare da Shugabannin Miyetti Allah a ranar Alhamis, sun cimma yarjejeniyar da ake ganin za a iya samar da zaman lafiya, a lokacin da rigimar ke neman tayar da hayaki har a nan Arewacin Najeriya.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Oyo, Ismail Adeleke, ya bayyana cewa gobarar ba ta yi asarar rayuka ko daya ba.

Ya ce ta cinye mashiga cikin gidan da matakalar bene baki daya da kuma babban daki da falo.

Cikin kayan da aka yi asara a cewar sa har da tebura, kujeru, babbar talbijin da wasu kayyaki.

Ya ce sun fara binciken musabbabin tashin gobarar.

Gidan dai ya na daya daga cikin gidajen da Igboho ya mallaka, kuma ba a ciki ya ke zaune ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Jigon Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi amfani da gogarma Sunday Igboho su ka ci zaben gwamnan jihar Ekiti a 2009.

Mashawarcin Siyasa na Shugaba Muhammadu Buhari, Babafemi Ojudu ne ya bayar da labarin, wanda ya bayyana cewa da shi aka yi ruwa da tsakin yadda aka yi murda-murdar tare da Igboho. Kuma ya ce shi ne ma ya hada shi da Tinubu.


Source link

Related Articles

81 Comments

  1. Thank you for another magnificent post. Where else may anyone get that type of information in such an ideal manner of writing?
    I have a presentation subsequent week, and I’m on the search for such info.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button