Labarai

Gumi yayi kakkausar jan kunne ga waɗanda suka kashe Deborah, ya ce ba hurumin su bane yanke hukuncin kisa don an zagi Annabi SAW

Babban malamin musulunci dake Kaduna Ahmed Gumi yayi kakkausar suka ga ɗaliban da suka kashe Deborah Samuel wacce aka kashe saboda zargin yin suka ga Annabi SAW.

A wata doguwar wa’azi da yayi wanda ya saka a shafinsa ta Facebook Gumi ya ce maimakon su dauki wannan hukunci na kashe Deborah hukumar makarantar ya kanata su kai kararta daga nan kuma sai akai gaba.

Hakazalika ya caccaki malaman da suke halatta kisa idan an Zagi Annabi SAW, yana mai cewa gaba dayan su basu fahimci ayoyi da hadisan da suke dogaro da su bane sannan kuma suna ingiza mutane ne akan abinda basu da ilimi akai.

” Don an Zagi manzon Allah, ba a baka dama ka kashe mutum ba, wannan hurumi ne na hukuma, idan ka yi haka kai ma ka aikata laifi.

” Idan Deborah ta Zagi Annabi, kamata yayi a kai karanta wajen hukumar makarantar, daganan kuma sukai ga sultan sannan gwamnati ta shiga ciki, amma ba kawai ku suntumi makamai ba ku kashe ta.

Gumi ya ce duk wani malami da ke cewa wai ayi haka don an zagi Annabi SAW, ba su san abinda suke yi ba.

” Kawai sai kaji wasu da na ta jawo ayoyi da hadisai amma basu san su da fassarar su ba yadda yakamata.

” Idan hukuma bata ɗauki mataki ba wannan ba huruminka bane. Hukuma ne bata dauki hukunci ba, kuma ita kanta hukumar ma tana da damar wasu dalilai ya hana ta yanke wasu hukuncin.

Ɗaliban kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto sun kashe wata ɗaliba da ake zargin ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.

Bayan haka abin ya kawo tarzoma da zanga-zanga a garin Sokoto inda har yakai ga an saka dokar hana walwala a awa 24.

Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta yi kama wasu mutum biyu da ake zargi hannu wajen kisan Deborah.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. Hi there, i read your blog from time to time and i own a similar one and i was just wondering if you get
    a lot of spam feedback? If so how do you protect against it, any
    plugin or anything you can recommend? I get so much lately it’s driving me insane so any assistance is very much appreciated.

    My web-site … career path

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news