Labarai

Gwamna Badaru ya tare a Abuja, ya yi watsi da aikin cigaban al’ummar Jigawa – Ahmed

Mansur Ahmed, maitamakawa Tsohon Gwamnar Jihar Jigawa, Sule Lamido, kan harkar yada labarai yayi kaukausar suka ga gwamnatin APC mai mulki a Jigawa cewa gwamnatin karkashin gwamna Abubakar Badaru tayi watsi da bukatun al’ummar jihar inda shi gwamnan ya tare a Abuja kawai, daga hidimar uwar jam’iyyar sa ta APC, sai hidimar shugaba Muhammadu Buhari aiki ya ke yi, Jigawa kuwa Ko’Oho.

” Anyi ittifakin cewar duk gwamnonin Kasar nan babu wadda ya kai Badaru kiran sunan Buhari da kokarin bashi kariya a kowanne lokaci amma kuma duk gwamnonin Kasar nan babu wadda bai ci ribar gwamnatin Buhari ko soyayyar Buhari a jiharsa kamar Badaru ba, babu wani aikin raya kasa na Naira biliyan 20 da Buhari ya yiwa jihar Jigawa wadda za’a ce duk Najeriya mu kaɗai aka yiwa shi ko a Jigawa aka fara shi.

” Shi kaɗai ne gwamna ɗaya tilo da har yau bana tunanin ya yiwa wani ɗan asalin Jigawa sanadin muƙami ko wata kujera a gwamnatin Buhari da za’a iya dagawa ayi tunkaho da ita, in kaga Jigawa da kujera to an bawa kowacce jiha irinta, duk ɗan Jigawa da ka gani da muƙami a gwamnatin Buhari ko kaga ya bashi muƙami ba ta sanadi ko sa hannun Badaru bane shi yasan ta inda ya samu muƙaminsa ko ɗan wata jihar ne yayi masa hanya.

” A shekaru 6 da Buhari yayi yana mulkin kasar nan sau biyu rak yazo Jigawa ɗaya kaddamar da kayan gona da Mangoro da sauransu ɗaya kuma yaƙin neman zaɓen tazarce amma Badaru ya je Villa ya fi sau shurin masaki ko a gayyata, ko a rakiya ko kuma an daukko wani aiki da ake ganin sauran gwamnoni baza su yi ba suna zaune a jihohinsu suna yiwa al’umma aiki shi sai a bashi yayi.

“Kullum yana hanyar yiwa Buhari da APC aiki daga can sai can ya kasa samun nutsuwa ya zauna a Jigawa yayi wani aikin raya ƙasa guda ɗaya da zai kai Naira biliyan goma wadda idan ya bar gwamna za’a gani a tuna dashi, aiyyuka masu sauki da araha ma irinsu aikin Asibitin Birnin Kudu yau shekara shida sun kasa kammaluwa, Asibitin Hadejia Specialist shekara biyar an kasa bikin budewa, banda sauran alkawura na Asibitoci.

” In Badaru ya ɗora alhakin rashin tsaro a tattaunawarsa da Channels akan gwamnatin baya ta mulkin PDP babu laifi tunda a lokacin mulkinta ne aka fara Boko Haram amma garkuwa da mutane, talauci haram, fatara haram, yunwa haram, tsadar rayuwa haram, kone garuruwan al’umma da kisa marar dalili kuma ai a mulkin Buhari aka same su ko?

Kamata yayi Badaru ya mayar da hankali wajen nemowa Jigawa aiyyukan raya ƙasa da zasu ciyar da ita gaba a gwamnatin tarayya amma ba mu yi ta ganinsa yana yawon aikin Jam’iyya ko aikin Buhari ba tunda Jam’iyyar wa’adinta ya taho karewa al’ummar kasa sun gamsu cewar banda zance da alkawuran da baza a iya cikawa ba babu abinda APC za ta yi musu asali ma sun gwammaci ta mayar dasu inda ta daukko su a mulkin baya na PDP.

PREMIUM TIMES HAUSA ta nemi daga bakin kakakin gwamna Badaru Auwal Sankara amma lambar ba ta zuwa, haka shima kwamishan yada labarai Bala Ibrahim, wayar sa bata shiga a lokacin rubuta wannan labari.

Idan ba a manta ba gwamna Badaru ya bayyana cewa a lokacin da yake hira da gidan talbijin din Channels cewa ita kanta hare-haren yan bindiga da satar mutane gadon ta Buhari yayi da ga gwamnatocin baya.

” Ina so yan Najeriya su sani cewa hare-haren yan bindiga, garkuwa da mutane da Boko Haram, duk daga gwamnatocin baya na PDP Buhari ya yi gadon su. Kuma idan ba a manta ba Buhari ya dare kujerar mulki a lokacin kananan hukumomi da dama ke karkashin ikon Boko Haram, amma yanzu duk sum zama tarihi. ” in ji Badaru a hirar sa da Channels.


Source link

Related Articles

126 Comments

 1. Yesterday, while I was at work, my sister stole my iPad and tested to see if it can survive
  a 40 foot drop, just so she can be a youtube sensation. My
  apple ipad is now broken and she has 83 views. I know this is totally off topic but I had to share it with someone!

 2. Oh my goodness! Awesome article dude! Thank you so much, However I am having
  troubles with your RSS. I don’t understand the reason why I cannot join it.

  Is there anybody else having the same RSS issues? Anyone who
  knows the answer can you kindly respond? Thanx!!

 3. Hello everyone, it’s my first visit at this web site, and post
  is genuinely fruitful designed for me, keep up posting these types of articles or reviews.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button