Ciwon Lafiya

Gwamnati za ta saka wadanda basu cikin tsarin Inshorar Lafiya a Kasar nan

Gwamnatin Najeriya Karkashin ma’aikatar Kiwon Lafiya ta bayyana cewa ta kirkiro wani tsari da zai sa wadanda basu cikin tsarin Inshorar lafiya ta kasa su samu shiga.

Wannan tsari na inshoran lafiya da gwamnati ta kirkiro zai saka mutum da iyalansa da kuma dan uwan sa kai tsaye.

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya sanar da haka a taron kaddamar da shirin da aka yi a otel din Transcorp Hilton a Abuja.

Idana ba a manta a shekarar bara wato, 2019, Shugaban Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta kasa (NHIS) Mohammed Sambo ya bayyana cewa Najeriya za ta iya cimma nasarar samar wa ‘yan Najeriya kiwon lafiya na gari a farashi mai sauki ga kowa da kowa idan ta tilasta wa mutanen shiga tsarin inshoran kiwon lafiya ta kasa.

Ya ce tilasta wa mutane shiga tsarin hanya ce da za a rika samar da isassun kudaden domin isar da shirin ga wadanda basu ciki.

Sambo yace za a samu nasarar haka ne idan aka yi dokar da ta kafa hukumar Inshorar Kiwon Lafiya garambawul.

Tuni dai har majalisar dattawa ta mika wa shugaba Muhammadu Buhari gyarar kudirin da ta kafa hukumar domin a maida ita doka. Sai dai kuma har yanzu shugaba Buhari bai saka hannu a kai ba.


Source link

Related Articles

96 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button