Ciwon Lafiya

Gwamnatin Buhari ta ƙakaba sabbin harajin kira na wayar hannu ga ƴan Najeriya

Gwamnatin Najeriya za kirkiro sabbin harajin kira na wayar salula a samu karin kuɗin da za a rika kula da talakawa da gajiyayyu kiwon lafiya

Shugaba Buhari ya ce gwamnati na kokarin ganin ta saka akalla talakawa da gajiyayyu miliyan 83 a cikin tsarin inshorar lafiya ta ƙasa.

Sakamakon binciken da NOI Polls ya gudanar ya nuna cewa mutum 8 daga cikin mutane 10 a Najeriya basu cikin tsarin inshorar lafiya sannan mafi yawan ‘yan Najeriya na kashe kudi idan suka je asibiti.

Gwamnati ta ce za ta rika karban harajin Kobo daya akan kowani sakan na waya da mutane za su rika yi ta saka su a asusun da ta bude domin tallafa wa kuwo lafiyar talakawa a kasar nan.

Gwamnati ta kuma ce za ta rika zuba Wani kaso daga cikin Kashi daya da take amsa domin inganta fannin lafiyar kasar nan, harajin da take karba na inshorar lafiya, harajin daga jari, tallafi da sauran su a cikin asusun.

Talakawa da gajiyayyun da asusun zai rika taimakawa sun hada da Yara kanana ‘yan ƙasa da shekara biyar, mata masu ciki, tsofaffi, masu tabuwar hankali da sauran su.

Sashe na 26 na dokar inshorar lafiya ya ce gwamnati za ta nemi kudi domin Samar wa talakawa da gajiyayyu kiwon lafiya ta hanyoyin da kwamitin zantaswa za ta amince da su.

Idan gwamnati ta fara amfani da wannan doka mutane da dama dake amfani da wayoyin salula za su ga Karin kudi a farashin waya da aikawa da sakonin tes da suke yi.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button