KannyWood

Gwamnatin Kano ta haramta shirya fim kan kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya

GWAMNATIN Jihar Kano ta haramta shiryawa ko nuna duk wani fim da aka yi shi a kan yadda ake garkuwa da mutane ko sayarwa da shan kayan maye ko ƙwacen waya.

Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana wa mujallar Fim cewa an yi wannan dokar ne domin kare mutunci da tarbiyyar mutanen Jihar Kano.

Ya yi nuni da cewa ba waɗannan finafinan ake da buƙata ba a yanzu domin kuwa akwai labarai da dama waɗanda ya kamata masu shirya finafinai su maida hankali a kan su.

Afakallah ya ce, “Wannan doka an yi ta ne domin kare duk wani abu na mutunci da kuma tarbiyyar mutanen Jihar Kano, kuma da man can akwai wannan doka.

“Akasarin finafinan da ake shiryawa ana shirya su ne domin su faɗakar, su wa’azantar, to kuma idan aka kalli tsarin finafinan, wasu sun bauɗe daga hanya, an fara koya wa mutane maimakon su faɗakar sai su koyo munanan ɗabi’u. Wannan ya sa dole a tashi a ɗauki mataki.”

Shugaban ya faɗa da kakkausar murya cewa hukumar sa ta taka wa shirya irin waɗannan finafinan burki.

Ya ce, “Mun taka burki da duk wani fim da za a shirya shi da za a nuna makamai a ciki saboda irin halin da mu ke ciki a yanzu domin daƙile yaƙi da ta’ammali da makamai a cikin al’umma.

“Hukumar Tace Finafinai ta hana dukkanin wani fim da za a yi wanda zai nuna hada-hada da kuma ta’ammali da ƙwayoyi ko sayar da su ko shan su.

“Sannan bayan wannan da abubuwan da ake yi na garkuwa da ɗan’adam, yadda ake yi da kuma yadda abubuwan su ke kasancewa.”

Bugu da ƙari, Afakallah ya ce, “Shi kan sa nuna ƙwacen waya da ake yi a cikin fim da sauran su, shi ma mun taka masa burki.”

Ya ce duk waɗannan abubuwan ba su ya kamata yanzu masu sana’ar shirya fim su maida hankali a kan su ba, domin akwai abubuwa da yawa na labarai da za a ɗauka waɗanda za su taimaki al’umma, misali maganar ilimi da maganar hana barace-barace da ake yi da gararambar yara a kan titi, zaman kashe wando da tumasanci.

“Duk waɗannan abubuwan ya kamata a maida hankali wajen shawo kan su,” inji shi.

Shugaban ya ce, “Yanzu hukumar mu ta tace finafinai daga wannan karon duk wanda zai yi wani fim da zai nuna shaye-shaye ko safarar su ko kuma kidinafin ko fito da makamai ana harkar daba ko ana wani abu, wannan abin mun taka masa burki.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button