Nishadi

GWANJA YA KIRA RUWA: NBC ta haramta wakar ‘Warr’ ta ce wakar bata tarbiyya ce

Hukumar kula da kafafen sadarwa NBC ta haramta waƙar ‘Warr’, wanda mawaƙin Hausa Ado Gwanja ya yi kuma ya karaɗe gidaje da shafukan mutane musamman ƴan yankin Arewa.

A sanarwar da NBC ta fitar wanda BBC HAUSA ta buga ta ce waƙar akwai rashin tarbiya da rashin kunya a cikin kalaman waƙar.

Hukumar ta ce a cikin waƙar akwai kalamai na zagi karara da nuna gurbatar tarbiyya inda ake nuna wasu suna barankaɗewa da kwalaben giya suna tangaɗi suna keta ashar.

Ado Gwanjo ya shahara wajen yin wakokin mata wanda suka yi fice.

Da yawa daga cikin wakokin akan yi ikirarin cewa wakokine dake bata tarbiya. Ƴan mata da matan aure kan sheke ayarsu da irin waɗannan wakoki musamman na Gwanja.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu mazauna garin Kaduna, Zaria da Kano musamman iyaye kuma dukkan su sun nuna amincewar su da dakatarwarbda NBC ta yi wa wakar Warr.

” Ni uwace amma tsakani da Allah, na yi matukar farincikin hana saka wannan waka, ‘ Warr’ sunan wakar kanta akwai shakiyanci a ciki. Sai kaga yara na bobbotsarewa wai suna wakar Gwanja. Wannan wani irin bata tarbiyya ce.

” Ba ƴan mata ba kawai, hatta matan aure ma sun lalace da sauraren irin waɗannan wakoki, Warr, Chass, duk na shakiyanci da bata tarbiyya. Sai kaga sharbebiyar mata ta na tiƙa rawa ko ina a jikinta na rawa wai tana rawar wakar ‘ Warr’ ko’ ‘Chass’.” In ji Hajiya Hassana.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news