Nishadi

Hadiza Gabon ta bayyana a Kotu, ta ce ba ya san mutumin da ya ce ta wawushe masa dubban nairori ba

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Wani ma’aikacin gwamnatin jihar Zamfara, Bala Musa ya maka fitacciyar ƴar wasa, Hadiza Gabon a kotun Shari’a dake Kaduna bisa zargin karya alkawarin aure da suka yi.

Musa ya ce sai da ya kashe ma Gabon naira 396,000 ɗawainiya da ya riƙa yi da ita.

Ya kamata Hadiza da Musa su gabata a kotun sranar Litini amma sai ita ba halarci zaman kotun ba.

A kotun Musa ya ce ya daɗe yana soyayya da Hadiza , a dalilin haka ne ya sa har suka yi wa juna alƙawarin aure.

“Daga lokacin da muka fara soyayya na kashe mata Naira 396,000. Duk lokacin da ƴan buƙatun sa suka taso ni ne nake biya mata su.

“Hadiza ta ki zuwa wurina a Gusau bayan mun kammala Shirin cewa za ta kawo min ziyara daga nan mu fara shirin aure.

Kotun ta fara shari’a ranar 23 ga Mayu amma a lokacin Hadiza bata a kotun.

Lauyan dake kare Hadiza Mubarak Kabir ya ce Hadiza ba ta zo kotun ba saboda ba ta da tabbacin ko sammacin da kotun ta aiko na gaske ne.

Kabir ya ce bisa ga irin aikin da Hadiza take yi dole ta riƙa taka tsantsan wajen irin mutanen da suke cewa sun santa ko kuma wata alaka ya shiga tsakanin su.

Ya ce kotu ta bashi dan wani lokaci domin ganin Hadiza ta zo kotun a zama na gaba.

Alkalin kotun Rilwanu Kyaudai ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 13 ga Yuni.

A ranar Talata, Gabon ta halarci zaman kotun inda ta bayyana cewa bata taba ganin wannan mutum ba, kamar yadda Daily Trust ta buga.

” Ni ban san shi ban taba haɗuwa da shi ba.”

Lauyan Gabon ya ce ” mutumin ya yi ta yin hira da wani ne a shafukan da wasu suka buɗe na ƙarya a yanar Gizo zo mai dauke da hoton jarumar.

” Daga nan ne suka yaudare shi acewa Gabon ce ke hira da shi har suka wafce mai naira 300,000.

Sai dai kuma lauyan mai shigar da ƙara ya ce ba haka bane Gabon ce da kanta suka yi ta murza soyayya da har ta ci masa kuɗi.

Alkalin kotun ya ɗage shari’ar zuwa 28 ga wannan watan.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button