Labarai

HARƘALLAR KWANGILA: EFCC ta kama Patricia Etteh, tsohuwar Kakakin Majalisar Tarayya

Hukumar EFCC ta tsare Patricia Etteh, tsohuwar Kakakin Majalisar Tarayya, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen kwangila.

Etteh ta yi shugabancin Majalisar Tarayya na taƙaitaccen lokaci, daga watan Yuni 2007, zuwa Oktober 2007.

EFCC sun kama ta ne ranar Talata a Abuja, bisa zargin karɓar naira miliyan 130 daga hannun wani ɗan kwangilar ayyukan samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta, a jihar Akwa Ibom.

Kwangila ce dai wadda aka bai wa wani kamfani mai suna Phin Jin Project Limited, a cikin 2011 ta naira miliyan 240.

Premium Times ta yi bincike a jerin sunayen kamfanonin da Hukumar Rajistar Kamfanoni ta yi wa rajista, wato CAC, amma ba ta ga sunan kamfanin ba.

Masu bincike sun ce makonni bayan an bai wa ɗan kwangilar kuɗaɗen somin-taɓin fara aiki, ya tura wa Etteh naira miliyan 130, alhakin kuma ita ba darakta ko wata mai hannun jari ba ce a kamfanin.

“Biyan waɗannan kuɗaɗen masu yawa haka a cikin Asusun Patricia Etteh ya haifar da zargin ta da ake yi.

“Ta yi iƙirarin cewa kuɗaɗen da ɗan kwangilar ya tura a cikin asusun ta, biyan bashi ne ya yi mata daga wasu kuɗaɗen da ta taɓa ramta mata. Don haka mu na bibiya da kuma binciken gaskiya ko rashin gaskiyar iƙirarin na ta.

“Saboda wani abin lura kuma shi ne yadda aka kandami wasu ƙarin miliyoyin kuɗaɗe aka ɗora a kan kuɗaɗen kwangilar a lokacin da za a biya kwangilar.

“Naira miliyan 240 ya kamata a fitar, amma sai aka biya Naira miliyan 287. Dalili kenan mu ke so ita da ɗan kwangilar su fayyace mana wannan asarƙala.”

Sannan kuma EFCC ta yi zargin cewa ɗan kwangilar bai yi aikin da aka ba shi ɗin ba, duk kuwa da cewa an biya shi kuɗaɗen.” Inji majiyar cikin hukumar.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. My spouse and I stumbled over here different page and thought I may as well check things out.
    I like what I see so now i am following you.
    Look forward to looking over your web page repeatedly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button