Labarai

HARIN JIRGIN ƘASA: A gaggauta ceto Azurfa John daga hannun ‘yan ta’adda kafin su yi mata auren-dole – Mamu

Jim kaɗan bayan ‘yan ta’addar da su ka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun ƙara sakin fasinjoji huɗu, mai shiga tsakani Tukur Mamu ya yi kiran gaggawa cewa Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa CAN su gaggauta ceto rayuwar wata budurwa da ke cikin sauran fasinjojin da ke hannun su.

Mamu ya ce an sanar da shi su na da niyyar yi mata auren-dole da wani daga cikin ‘yan ta’addar da aka ce “ya na mutuwar son ta.”

Cikin sanarwar da Mamu ya aika wa PREMIUM TIMES, ya ce waɗanda aka saki ɗin su huɗu, sun kai ziyara ofishin sa a Kaduna, inda su ka yi masa godiya dangane da shiga tsakanin da ya yi, inda ya riƙi ‘yan ta’adda su janye barazanar kisa da su ka yi wa, fasinjojin a baya.

Daga cikin waɗanda aka saki ɗin a ranar Juma’a, har da wata gyatuma mai shekaru 90, wato Halimatu Atta, wadda ta fi dukkan sauran fasinjojin yawan shekaru.

A cikin takardar da Mamu ya aika wa PREMIUM TIMES, ta ce a yanzu sauran mutum 23 a hannun masu garkuwar.

Sauran uku da aka saki a ranar Juma’a sun haɗa da ‘yar gyatuma Halimatu, mai suna Adama Atta Aliyu, mai shekaru 53.

Sai kuma Mohammed Sani Abdulmajid, wanda tun farkon kama fasinjojin shi ne ya yi tunanin bada shawarar masu garkuwar su tuntuɓi Mamu domin ya shiga tsakani.

Sai kuma Alhaji Modin Modi Bodinga, wani mutumin Sokoto.

Da ya koma kan halin da Azurfa John ke ciki kuwa, Mamu ya ce ya kamata CAN ta hanzarta, kuma kada ta maida lamarin Azurfa siyasa, ta yi ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ita.

Ya ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta, domin sauran fasinjojin 23 da ke tsare, su na cikin wani mawuyacin hali.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news